2019: ‘Yan Najeriya sun yiwa Atiku shagube a kan zubar da hawaye

2019: ‘Yan Najeriya sun yiwa Atiku shagube a kan zubar da hawaye

- A satin da ya gabata ne tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zubar da hawaye, yayin da ya yanki tikitin neman PDP ta tsayar da shi takarar shugaban kasa.

- Hawayen da Atikun ya zubar ya jawo barkewar cece-kuce da tsokana a tsakanin ‘yan Najeriya musamman masu ra’ayin siyasa.

- Rahotanni sun bayyana cewar jam’iyyar PDP ta cinma yarjejeniya da dukkan ‘yan takarar shugaban kasa cewar zasu goyi bayan dukkan wanda ya yi nasara a zaben fitar da gwani

A cikin satin da ya gabata ne tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bawa ‘yan Najeriya mamaki bayan ya zubar da hawaye yayin da ya je karbar takardar takarar neman tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP.

Batun zubar da hawayen da Atikun ya yi ta jawo barkewar cece-kuce da tofa albarkacin baki daga ‘yan Najeriya, musamman a dandalin sada zumunta.

2019: ‘Yan Najeriya sun yiwa Atiku shagube a kan zubar da hawaye
Atiku yana share hawaye
Asali: Facebook

Wasu masu shagube na ganin cewar kukan na Atiku kan iya bashi nasara a zabe kamar yadda ta faru da shugaba Buhari kafin ya zama shugan kasar Najeriya. Sai dai masu wannan ra’ayi sun ce amma fa sai bayan shekara 4 zai zama shugaban kasa tunda shugaba Buhari ma bai zama shugaban kasa ba sai a shekarar 2015, bayan tun 2011 ya yi kuka.

DUBA WANNAN: 2019: PDP zata kori 'yan takara masu kunnen kashi

A wani bangaren, wasu na ganin cewar Atiku ya zubar da hawaye ne saboda mai yiwuwa wannan shine lokaci na karshe da yake dashi na samun dammar yin takarar shugaban kasa, musamman idan aka yi la’akari da shekarun sa na haihuwa.

Wani sashe na jama’a a dandalin sada zumunta sun zargi Atiku da kakalo hawayen domin jan hankali da kuma samun tausayi daga masu zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel