Dan takarar shugaban kasa a PDP ya roki yan Nigeria da su yi karo-karo don saya masa tikitin tsayawa takara

Dan takarar shugaban kasa a PDP ya roki yan Nigeria da su yi karo-karo don saya masa tikitin tsayawa takara

- Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Malam Hamidu Tafida, ya roki yan Nigeria da su saya masa takardar tsayawa takarar fitar da gwani

- Yana rokon yan Nigeria akalla Miliyan daya, da su yi masa karo karon Naira 200 don saya masa tikitin tsayawa takara

- Tafida ya yi alkawarin samar da ayyukan yi ta hanyar bunkasa fannin noma da samar da masana'antu, idan har aka zabe shi a 2019.

A ranar asabar, 1 ga watan Satumba, Malam Hamidu Tafida, wanda ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, ya roki yan Nigeria da su yi masa karo karon 200 kowanne, don bashi damar siyen tikitin tsayawa takara.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ta ruwaito cewa, Tafida ya yi wannan roko ne a Jalingo ya yin da ya ke kaddamar da kudurinsa na tsayawa takarar shugaban kasar.

NAIJ.com ta tattara rahoto cewa yanayin da kasar ta ke a ciki na bukatar sadaukarwa daga dukkanin yan Nigeria don ganin komai ya daidaita a kasar.

KARANTA WANNAN: Ruwan sama ya rusa makabarta da hana mutane binne gawa a jihar Katsina (Hotuna)

Dan takarar shugaban kasa a PDP ya roki yan Nigeria da su yi karo karo don saya masa tikitin tsayawa takara

Dan takarar shugaban kasa a PDP ya roki yan Nigeria da su yi karo karo don saya masa tikitin tsayawa takara
Source: Depositphotos

"A yau ina farin cikin sanar da kudurina na tsayawa takarar shugaban kasar Nigeria. Bari na yi amfani da wannan damar, in roki akalla yan Nigeria Miliyan daya, da su yi karo karo na Naira 200 kowanne, su saya min tikitin tsayawa takara don bani damar cika alkawuran da na dauka" a cewar sa.

Tafida, wanda mataimakin darakta ne a karamar hukumar Jalingo da ke jihar Taraba, ya yi nuni da cewa, ya zamarwa yan Nigeria dole su kauracewa batagarin yan siyasa, don ganin dprewar ci gaban kasar.

Ya ce idan har haaka zabe shi, zai magance cin hanci da rashawa da kuma matsalar tsaro da tayiwa kasar katutu, kana zai samar da hanyoyin ci gaba a kasar. Dan takarar ya kuma yi alkawarin samar da ayyukan yi ta hanyar farfado da masana'antu da kuma bunkasa fannin noma.

Ya shawarci al'umma da su yaki mummunar akidar nan ta siyen kuri’u, ya na mai cewa irin wannan dabi’a ce ke gurguntar da kasar.

Labari Makamancin wannan:

A baya bayan nan NAIJ.com ta ruwaito cewa jam’iyyar PDP ta kasa, a ranar litin, 27 ga watan Augusta, sun sanar da fara saita tikitin tsayawa takarar fitar da gwani ga mambobinsu da ke da sha’awar tsayawa takarar a matakai dab-daban, a fuskantar zaben 2019 da ke gabatowa.

Jam’iyyar ta yi wannan sanarwa ne ta hannun Sakataren tsare tsare na jam’iyyar a matakin kasa, Col. Austin Akobundu (mai ritaya) a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kallo ya koma sama: Kasashen duniya sun tsoma baki kan zaben jihar Osun

Kallo ya koma sama: Kasashen duniya sun tsoma baki kan zaben jihar Osun

Kallo ya koma sama: Kasashen duniya sun tsoma baki kan zaben jihar Osun
NAIJ.com
Mailfire view pixel