2019: Samuel Ortom ya yanki Tikitin takara ta kujerar Gwamnan jihar Benuwe

2019: Samuel Ortom ya yanki Tikitin takara ta kujerar Gwamnan jihar Benuwe

Mun samu cewa gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya yanki tikitin takara ta neman tazarcen kujerar sa a yayin zaben 2019 karkashin jam''iyyar adawa ta PDP kamar yadda shafin jaridar Vanguard ta ruwaito a yau Asabar.

Kakakin fadar gwamnatin jihar, Terver Akase, shine ya bayyana hakan yayin da gwamnan ya yanki tikitin sakamakon ci gaba da karatowar zaben fidda gwani na jam'iyyar.

Gwamnan ya mika godiyar sa ga shugabanci da kuma mambobin jam'iyyar dangane da ba shi dama ta yankar tikitin jam'iyyar domin fafafatawa a babban zabe na 2019.

2019: Samuel Ortom ya yanki Tikitin takara ta kujerar Gwamnan jihar Benuwe

2019: Samuel Ortom ya yanki Tikitin takara ta kujerar Gwamnan jihar Benuwe
Source: UGC

Ya kuma yabawa magoya bayan sa na jihar tare da gargadin su akan ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin su gami da kawar da gaba da kiyayya ta bambance-bambancen akidu na siyasa.

KARANTA KUMA: Yadda wani mai cajin Waya ke samun N180, 000 a kowane wata

Kazalika gwamnan ya kuma mika godiyar sa ga al'ummar jihar sakamakon kwarara addu'o'i da fata na gari a garesa, inda ya sha alwashin ba zai kunyata su ba.

Jaridar NAIJ.com ta kuma ruwaito cewa, ambaliyar ruwa ta salwantar da rayukan mutane 14 a jihar Neja dake Arewacin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta-leko-ta-koma: Shugaba Buhari ya kwace Naira biliyan 14.9 din da ya ba wata jihar Arewa

Ta-leko-ta-koma: Shugaba Buhari ya kwace Naira biliyan 14.9 din da ya ba wata jihar Arewa

Ta-leko-ta-koma: Shugaba Buhari ya kwace Naira biliyan 14.9 din da ya ba wata jihar Arewa
NAIJ.com
Mailfire view pixel