2019: An gano hanyar da Saraki ke shirin amfani da ita don kayar da Buhari

2019: An gano hanyar da Saraki ke shirin amfani da ita don kayar da Buhari

- Kwararen dan jarida, Mr Dele Momodu, ya ce Bukola Saraki zai iya lashe zaben 2019 cikin sauki muddin aka tsayar dashi

- A cewarsa Saraki zai mayar da hankali ne wajen neman kuri'un jihohin Arewa ta tsakiya, a jihohin Arewa maso yamma kuma ya nemi samun 25%

- Ya kuma ce Saraki zai zabo mataimakinsa daga yankin Kudu maso gabas ko Kudu maso Kudu tunda samun kuri'un Yarabawa ba zai masa wahala ba

Kwararen dan jarida kuma marubuci, Dele Momodu, ya yi fashin baki kan dabarar da ya ce, shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki zai yi amfani da ita domin ya kayar da shugaba Muhammadu Buhari a babban zaben shekarar 2019.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Pendulum, Momodu ya ce da farko ya cire sunnan Saraki daga cikin 'yan takarar shugabancin kasa ne saboda la'akari da yankin da ya fito kasancewarsa dan asalin jihar Kwara.

2019: An gano hanyar da Saraki ke shirin amfani da ita don kayar da Buhari
2019: An gano hanyar da Saraki ke shirin amfani da ita don kayar da Buhari
Asali: Depositphotos

"Hanyar da Saraki zai bi domin samun nasara tana da sauki saboda Buhari zai yi amfani da dabarar da ya saba na cewa dan takarar da ya fito da Arewa maso yamma ne zai iya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya," kamar yadda Momodu ya rubuta.

DUBA WANNAN: Albashin gwamnonin Najeriya da kwamishinonin jihohi

Momodu ya cigaba da cewa, "Akwai matukar wahala wani dan takara daga Arewa maso yamma ko Arewa maso kudu ya kayar da Buhari duk da cewa PDP suna da 'yan siyasa kwararu wanda suka cacanta. Abinda ake bukatar shine dan takara da zai mamaye Arewa ta tsakiya kuma ya kasance dan yankin ne.

"Yana ganin bata lokaci ayi kokarin ja da Buhari a yankinsa na Arewa maso yamma kawai abinda ake bukata shine kashi 25% na kuri daga jihohin yankin. PDP ta mayar da hankalinta wajen tattaro jama'a daga sauran yankuna hudu cikin yankuna shida da muke dashi a Najeriya.

"Idan PDP ta tsayar da dan takarar da jama'a basu amince dashi ba, Buhari zaiyi nasara. Batun mataimakin shugaban kasa kuma, ya kamata a dauko wani daga yankin Kudu maso gabas ko Kudu maso Kudu, tunda yana da Kudu maso yamma tasa ce."

Da yake amsa tambaya kan zargin rashawa da ake masa, Saraki ya ce "Wannan babban aiki ne a gaba na saboda ana ta yada jita-jita a kai na kuma hakan yasa wasu mutane suka rude suke tsamanin gaskiya ce."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel