Albashin gwamnonin Najeriya da kwamishinonin jihohi

Albashin gwamnonin Najeriya da kwamishinonin jihohi

- Gwamnonin Najeriya na daga cikin 'yan siyasa da ake biya kudin albashi mai yawa

- A kwanan nan ne hukumar rabon arziki ta kasa (RMAFC) tayi kwaskwarima a kunshin albashin gwamnonin Najeriya

- Bayan jagorancin gwamnati a matakin jiha, gwamnoni na juya akalar jam'iyya a jihohin da suke mulki

Gwamnoni na daga cikin 'yan siyasa da ake biya albashi mai tsoka a duk fadin duniya.

Duk da kwaskwarimar da hukumar rabon arziki ta kasa (RMAFC) ta yiwa kunshin albashin gwamnonin Najeriya, hakan bai hana su zama 'yan siyasa dake karbar kudi mafi tsoka ba a Najeriya.

Albashin gwamnonin Najeriya da kwamishinonin jihohi
Albashin gwamnonin Najeriya da kwamishinonin jihohi
Asali: Twitter

A sabon kunshin albashin gwamnoni, mataimakansu da kuma kwamishinoni da hukumar RMAFC tayi, ana biyan gwamna miliyan N2.2m, adadin da idan aka hada da wasu alawus-alawus ke kaiwa miliyan N5m duk wata. Alawus da ragowar wasu kudi da gwamnonin ke samu sun banbanta daga jiha zuwa jiha amma tsurar albashin duk daya ne.

DUBA WANNAN: 2018: Karuwan Najeriya sun yi watsi da Buhari, sun goyi bayan Saraki

Banbancin alawus a tsakanin jihohi ne ya saka sanin adadin kudin da gwamna ke samu a wata zai yi wuya.

Albashin mataimakin gwamnan a Najeriya Naira miliyan N2.11m duk wata yayin da kwamishina zai dauki miliyan N1.33m duk wata.

Duk da wannan adadi, an rage adadin albashin gwamnonin idan aka kwatanta da abin da ake na baya.

Sai dai da yawan 'yan Najeriya na ganin gwamnoni da mataimakansu da kuma kwamishinoni na rayuwa fiye da albashin su. Wasu na ganin cewar ba daga albashi gwamnoni da masu rike da mukamin siyasa ke samun kudi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel