Yadda wani mai cajin Waya ke samun N180, 000 a kowane wata

Yadda wani mai cajin Waya ke samun N180, 000 a kowane wata

Wani matashi da ya yaki zaman kashe wando da sana'arsa ta cajin waya a birnin Lafiya na jihar Nasarawa, Ibrahim Usman, ya bayyana cewa yana samun kimanin N180, 000 a kowane wata wajen cajin wayoyin mabukata da Jannareta.

Matashin dai ya bayyana cewa, ya ribaci matsananciyar rashin wutar lantarki da ta yi kamari a birnin na Lafiya, inda yake samun N180, 000 a kowane wata wajen wannan sana'a ta sa kamar yadda bayyana yayin ganawar da manema labarai a ranar Asabar ta yau.

A cewar sa, albarkar wannan sana'a ta cajin wayoyin da ababe masu amfani da wutar lantarki ta yi sanadiyar bude ma sa hanya ta neman abinci tare da janyo ma sa budi na arziki.

Duk da cewa ba ya farin ciki dangane da matsananciyar rashin wuta a birnin na Lafiya, sai dai ya bayyana cewa ko shakka ba bu yana samun babbar riba mai albarka a sakamakon wannan lamari.

Yadda wani mai cajin Waya ke samun N180, 000 a kowane wata
Yadda wani mai cajin Waya ke samun N180, 000 a kowane wata
Asali: Depositphotos

A yayin ci gaba da ganawar sa da manema labarai Usman ya kuma bayyana cewa, dangane da wannan lamari na rashin wuta, ya na samun kimanin N6, 000 a kowace rana wanda a lissafinsa yake samun N180, 000 bayan kwanaki 30.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya isa 'Kasar Sin da safiyar yau ta Asabar

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan matashi yana batar da N1000 wajen sayen man fetur da zai kunna injinsa na jannareta a kowace yayin da yake tashi da riba mai dumbin yawa.

A yayin da Usman ke yabawa abokanan huldarsa ta kasuwanci, yana kuma shawarta matasa akan su kaurace zaman banza ta hanyar rashin dogaro da aikin gwamnati a koda yaushe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel