Ruwan sama ya rusa makabarta da hana mutane binne gawa a jihar Katsina (Hotuna)

Ruwan sama ya rusa makabarta da hana mutane binne gawa a jihar Katsina (Hotuna)

- Ruwan sama da akayi kamar da bakin kwarya a garin Albasu dake jihar Katsina, ya shafe makabartar garin tare da zabtare hanyar zuwa kai matattu

- Wani ma'abocin kafar sada zumunta ta Facebook, Muhammad Aminu Kabir ya fitar da labarin faruwar hakan a shafinsa na facebook

- An roki gwamnatin jihar, masu hannu da shuni, dama daukacin al'umma da sukaiwa al'ummar garin daukin gaggawa

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu yanzu, ya bayyana irin tashin hankalin da al'ummar garin Albasu dake karamar hukumar Sabuwa, jihar Katsina suka tsinci kansu a ciki, sakamakon ruwan sama da akayi kamar da bakin kwarya a garin, wanda ya shafe makabartar garin da hansu binne matattu.

Kamar yadda labarin faruwar hakan ya karade kafafen sada zumunta na yanar gizo, wakilin Legit.ng Hausa ya zanta da wani makusanci da yankin da abun ya faru, Muhammad Aminu Kabir, wanda kuma ya fara dora labarin afkuwar lamarin a shafinsa na Facebook.

KARANTA WANNAN LABARIN: Asiri ya Tonu: Yadda wani barawo ke amfani da karfe wajen satar kudi a Fatakwal (Hotuna)

Ruwan sama ya rusa makabarta da hana mutane binne gawa a jihar Katsina
Ruwan sama ya rusa makabarta da hana mutane binne gawa a jihar Katsina
Asali: Original

Muhammad Aminu Kabir, ya bayyana a shafinsa cewa bayan da tsohuwar makabartar garin Albasu ta cika, wani bawan Allah ya bayar da gonarsa, sai dai hankalin kowa a garin ya tashi sakamakon ruwan saman da ya shafe makabartar da kuma zabtare hanyar zuwa kai mamata.

Ga dai labarin kamar yadda ya rubuta:

"Innalillahi Wainna Illaihir Raji'un.

Tashin Hankali Al-ummar Garin Albasu dake Cikin Karamar Hukumar Sabuwa ta Jahar Katsina suna gab da Rasa Makabartar su ko Hanyar Zuwa Makabartar Inda Ake Rufe Mamata.

Bayanai da suke Fitowa daga wannan Yankin suna nuni dacewa Bayanda Tsohuwar Makabartar tasu ta Cika sai wani Bawan Allah yabada wata Gonar Shi wadda aka Maida Makabarta, a Yanayin Damina da Ake Ciki Kuma Hanyar Zuwa Makabartar ta zabtare saboda zaizayar kasa.

Yanzu haka Dai duk sadda zaaje Rufe Gawa dole sai an Ratsa cikin kogi ko wannan Hanyar da Ruwa ya wanke.

Wannan Hanyar dai itace wadda Shi kanshi Dan Majalisar dake wakiltar Yankin yake Amfani da ita zuwa Gonar Shi wannan yake nuni dacewa yasan da ita Amma Kuma yakasa Kai koken ga Mahukunta Dan akawo ma Al-umma dauki."

A karshe Muhammad Aminu Kabir, kafar sada zumunta na yanar gizon, ya roki gwamnatin jihar, masu hannu da shuni a yankin, dama daukacin al'umma, da su kai dauki ga al'umar yankin da abun ya shafa, yana mai cewa "Makabarta dai Gidan kowa da kowa ne."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel