2018: Karuwan Najeriya sun yi watsi da Buhari, sun goyi bayan Saraki

2018: Karuwan Najeriya sun yi watsi da Buhari, sun goyi bayan Saraki

- Kungiyar karuwan Najeriya (NANP) ta bayyana goyon bayanta ga takarar shugaban kasar Bukola Saraki

- Kungiyar ta bukaci 'yan Najeriya su goyi bayan Saraki domin ya zama shugaban kasa a 2019

- Shugabar kungiyar, Tamar Tion, ta ce kasuwar da suke samu ta ragu tun bayan hawan Buhari mulki

Kungiyar karuwan Najeriya (NANP) ta bayyana goyon bayanta ga takarar shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, a zaben shugaban kasa na 2019.

Kungiyar tayi kira ga daukacin 'yan Najeriya da su goyi bayan Saraki domin ya zama shugaban kasar Najeriya a zaben shekarar 2019.

Kungiyar na wadannan kalamai ne a jiya, Juma'a, ta bakin, Tamar Tion, shugabar kungiyar ta kasa.

2018: Karuwan Najeriya sun yi watsi da Buhari, sun goyi bayan Saraki
2018: Karuwan Najeriya sun yi watsi da Buhari, sun goyi bayan Saraki
Asali: Twitter

Tion ta zargi gwamnatin shugaba Buhari a karkashin jam'iyyar APC da kokarin kassara sana'ar su ta karuwanci.

DUBA WANNAN: Har yanzu Musulmin arewa na karkashin mulkin mallaka - Sarki Sanusi

Karuwan sun bayyana cewar tun bayan hawan shugaba Buhari mulki a shekarar 2015 sana'ar su ke komawa baya saboda karancin kwastomas.

"Muna goyon bayan takarar Alhaji Saraki ne saboda shine mutumin da zamu iya yarda da shi. Najeriya na bukatar shugaba mai kwazo da zai kawo canji a zahiri ba wai kawai a baki ba," in ji Tion.

Sannan ta kara da cewa, "mun rasa kwastomas masu yawan gaske tun bayan hawan gwamnatin APC, yunwa na neman tagayyara mu saboda rashin ciniki.

"Zamu zaburar da dukkan 'ya'yan kungiyar mu dake jihohin Najeriya 36 domin goyon bayan Bukola Saraki."

A shekarar 2015 ne kungiyar karuwan ta kasa tayi shelar yin lalata da mambobin ta kyauta na tsawon kwanaki uku ga duk mai bukata domin murnar cin zaben shugaba Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel