Da duminsa: Wasu 'yan majalisar APC 3 sun fita daga jam'iyyar

Da duminsa: Wasu 'yan majalisar APC 3 sun fita daga jam'iyyar

- Wasu 'yan majalisar jiha a Osun sun sauya sheka daga APC zuwa ADP

- Sun fice daga APC ne saboda gwamna mai barin gado ya tursasa musu wanda zai gaje shi

- Sunce ba zasu amince da daniyya da babakere ba shiyasa suka fice daga jam'iyyar

A halin yanzu da ke shirye-shirye gudanar da zaben gwamna a jihar Osun, jam'iyyar APC mai mulki a jihar ta bayar ta sanar da cewa wasu 'yan majalisar jihar 3 sun sauya sheka zuwa Action Democratic Party (ADP) a yau Asabar 1 ga watan satumba.

Da duminsa: Wasu 'yan majalisar APC 3 sun fita daga jam'iyyar
Da duminsa: Wasu 'yan majalisar APC 3 sun fita daga jam'iyyar
Asali: Twitter

Wakilin Legit.ng da ke jihar Osun, Sola Adetona, ya ruwaito cewa wadandan suka fice daga jam'iyyar APC sune Hon. Debo Akanbi mai wakiltan Ede ta Arewa, Hon. Tajudeen Famuyide mai wakiltan Ilesha ta yamma da kuma Hon. Abdullahi Ibrahim mai wakiltan karamar hukumar Iwo.

DUBA WANNAN: Har yanzu Musulmin arewa na karkashin mulkin mallaka - Sarki Sanusi

Rahotanni sunce Ciyaman din jam'iyyar ya karbi 'yan majalisar a sakatariyar ADP da ke jihar.

A jawabin maraba da 'yan majalisar da magoya bayansu, Hon. Akabi ya ce: "Mun san tsarin jam'iyyar APC a jihar mu kuma munyi yarjejeniya da gwamna Aregbesola cewa idan ya kammala shekaru 8 ba zai zaba mana dan takara ba.

"Ba zamu amince da babakere da daniyya ba kuma wasu 'yan jam'iyyar APC zasu biyo mu ADP domin tabbatar da cewa Moshood Adeoti ya yi nasara a zaben ranar 22 ga watan Satumba."

Cikin wadanda suka hallarci taron harda dan takaran mataimakin gwamna a jam'iyyar ADP, Farfesa Adeolu Durotoye, Hon. Sunday Akere da Omooba Dotun Babayemi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel