Asiri ya Tonu: Yadda wani barawo ke amfani da karfe wajen satar kudi a Fatakwal (Hotuna)

Asiri ya Tonu: Yadda wani barawo ke amfani da karfe wajen satar kudi a Fatakwal (Hotuna)

- A cafke wani dan Nigeria a kokarin da yake yi na satar kudi daga akwatin bada tallafi

- An cafke mutumin ne yana amfani da wasu wayoyin karfe don bude akwatin

- Rahotanni sun bayyana cewa an cafke mutumin ne a wata majami'a da ke Fatakwal

Legit.ng ta ci karo da wani labari, na wani mutumi da aka cafke a wata majami'a dake garin Fatakwal, inda yake kokarin satar kudi a akwatin da aka tanadar don jama'a su rinka jefa tallafinsu.

Wannan labarin dai ya yadu a kafafen sada zumunta na yanar gizo, wanda wani ma'abocin kafar Facebook mai suna Ezekiel West Tamunominabo ya rubuta a shafinsa. Ma'abocin kafar ta Facebook, ya bayyana cewa an cafke mutumin ne a lokacin da yake kokarin bude kwadon akwatin da wasu wayoyin karfe.

Yadda wani barawo ke amfani da karfe wajen satar kudi daga akwatin bada tallafi a Fatakwal
Yadda wani barawo ke amfani da karfe wajen satar kudi daga akwatin bada tallafi a Fatakwal
Asali: Original

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: PDP ta bukaci wasu yan takar shugaban kasa a jam'iyyar da su janye kudurinsu - Majiya

A cewar Ezekiel, har zuwa lokacin da aka cafke mutumin, ya samu nasarar ciro Naira dari biyar ne daga akwatin. Ya ce limamin majami'ar yayiwa barawon addu'o'i shiriya bayan da mambobin majam'iar suka kama shi.

Haka zalika, daga labarin na Facebook, rahotanni sun bayyana cewa mutumin ya dade yana aikata irin wannan laifi. An taba samunsa da aikata makamancin laifin a wasu majami'u da dama.

Yadda wani barawo ke amfani da karfe wajen satar kudi daga akwatin bada tallafi a Fatakwal
Yadda wani barawo ke amfani da karfe wajen satar kudi daga akwatin bada tallafi a Fatakwal
Asali: Original

Ga dai rubutun da Mr. Ezekiel ya yi:

"An cafke wani mutumi yana sata a a majami'ar Anjelika ta St. Marks dake Fatakwal.

A safiyar yau ne a a majami'ar Anjelika ta St. Marks, aka cafke wani mutumi yana satar kudi a akwatin da mambobin majami'ar ke bada tallafi. Wanda zuwa lokacin da aka kamashi, ya samu nasarar satar Naira 500 ne daga akwatin, daga rahotannin da aka tattara, mutumin ya dade yana aikata wannan aika aikar, inda yake amfani da wayoyin karfe masu tsayi da kuma sanya danko a karshensu don kamo kudin.

Limamin majami'ar ya yi ma mutumin addu'o'i, wanda ya yi ikirarin cewa ya dade yana yin sata a majami'ar... Dama dai ance rana daya ta barawo ce, rana daya kuma ta mai kaya.

Rahoto daga Ezekiel Tomunominabo, yammacin Fatakwa"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel