Har yanzu Musulmin arewa na karkashin mulkin mallaka - Sarki Sanusi

Har yanzu Musulmin arewa na karkashin mulkin mallaka - Sarki Sanusi

Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi fashin baki kan yadda turawan mulkin mallaka suka ruguza ilimin Larabci da Ajami a Arewa kuma suke daukan masu wannan ilimin a matsayin jahilai. Sarkin ya yi kira da gwamnati da dauki matakin gyara saboda daraja ilimin addini da wasu harsuna da suka gabaci turancin.

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ce har yanzu Musulmin arewacin Najeriya suna karkashin mulkin mallaka ne duk da cewa Najeriya ta samu 'yancin kai shekaru 60 da suka gabata.

Sarki Sanusi ya fadi hakan ne saboda a cewarsa tun daga lokacin da aka samu 'yanci har yanzu, Najeriya ba ta amince da tsarin ilimin musulunci wanda aka kwashe shekaru 500 ana amfani dashi ba.

Har yanzu Musulmin arewa na karkashin mulkin mallaka - Sarki Sanusi
Har yanzu Musulmin arewa na karkashin mulkin mallaka - Sarki Sanusi
Asali: Twitter

Sarki Sanusi ya yi wannan maganar na a taron kaddamar da wani littafi da mai taken 'Makarantun koyan karatun Kur'ani a Najeriya' da taron jin ra'ayoyin jama'a kan wani fim da ake shiryawa mai taken 'Duniya Juyi-Juyi' wanda wani dan kasar Jamus, Hannah Hoechner ya ke shiryawa.

An gudanar da taron ne a ranar Laraba a dakin taro na tunawa da Aminu Kano da ke Mambayya House a jihar Kano.

DUBA WANNAN: Wata mace Kirista ta zama gwamna a kasar Misra a karon farko

Sarki Sanusi ya koka kan yadda har yanzu ake daukan wadanda su kayi karatun allo a matsayin 'jahilai' kuma ake kidayasu cikin wadanda basu zuwa 'makaranta'.

Ya kara da cewa bai dace a rika kiran almajirai jahilai ba tunda ilimi na nufin iya rubutu da karatu ne kuma sun iya rubutu da karatun larabci da ajami.

Kalmar Almajiri an samo ta ne daga harshen labarabci 'Al-Muhajirun' ma'ana wanda ya bar gidana domin neman ilimin addinin musulunci. Sai dai abin takaici shine yadda aka bari tsarin ilimin ya tabarbare yara suka koma barace-barace.

Sarki Sanusi ya janyo hankali kan tarihin yadda turawan mulkin mallaka suka ruguza ilimin addinin musulunci, 'wani mission, Rabarand Miller ya rubuta wasika zuwa Lord Luggard inda ya shawarce shi ya haramta amfani da Larabci da Ajami a gwamnatance."

Daga karshe Sarki Sanusi ya yi kira da gwamnati tayi garambawul a tsarin ilimin Najeriya ta yadda za'a bawa wasu harsunan daraja bai wai turanci kawai ba a maimakon yadda ake daukan duk wanda bai iya turanci ba a matsayin jahili.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel