Yadda aka tsige Shugabannin Majalisar Dattawa a lokacin Obasanjo

Yadda aka tsige Shugabannin Majalisar Dattawa a lokacin Obasanjo

Ganin yadda ake tarka-tarkar tsige Bukola Saraki daga Majalisar Dattawan Kasar nan. Mun kawo maku jerin wasu shugabannin Majalisar Dattawan da aka taba tsigewa a tarihin siyasar Najeriya daga shekarar 1999 zuwa yanzu.

Yadda aka tsige Shugabannin Majalisar Dattawa a lokacin Obasanjo
An sauke Shugabannin Majalisar Dattawa har 2 a farkon Gwamnatin Obasanjo
Asali: Facebook

Kawo yanzu dai an yi Shugabannin Majalisar Dattawa 7 bayan an dawo tsarin farar hula.

1. Cif Evan Enwerem

Sanata Cif Evan Enwerem ne Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya na farko bayan dawowar mulkin farar hula a 1999. Sai dai Sanatan bai dade ba ‘Yan uwan sa su ka tsige sa bisa zargin rashin gaskiya, aka nada Chuba Okadigbo wanda ya zo na biyu a zaben da aka yi.

KU KARANTA: An tsige shugabannin Jam'iyyar PDP a Jihar Kano

2. Dr Chuba Okadigbo

Bayan an sauke Evan Enwerem daga kujerar sa ne aka nada Chuba Okadigbo a 1999. Sai dai shi ma Chuba Okadigbo ya bar kujerar bayan wani 'dan lokaci. Shugaban Majalisar ya zargi Shugaban kasa na lokacin Olusegun Obasanjo da kokarin yin kutun-kutun na tsige sa.

Chuba Okadigbo dai yayi ta rikici har ta kai ya tsere da sandar Majalisar zuwa gidan sa, hakan ya jawo takaddama da ‘Yan Sanda har ta kai ya rasa kujerar sa a karshe. A wannan Majalisar ma dai an samu irin wannan rikici na dauke sandar girman Majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel