Matar Gwamna Abubakar ta sha alwashin yaƙar ta'ammali da muggan ƙwayoyi a jihar Bauchi

Matar Gwamna Abubakar ta sha alwashin yaƙar ta'ammali da muggan ƙwayoyi a jihar Bauchi

Mun samu cewa a ranar Juma'ar da ta gabata ne uwargidan gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Hadiza Abubakar, ta sha alwashin hada gwiwa da dukkanin masu ruwa da tsaki wajen yakar ta'ammali da muggan ƙwayoyi a fadin jihar.

Hajiya Hadiza ta sha wannan alwashi ne yayin rufe wani taron kwanaki biyu da aka gudanar kan yaki da ta'ammali gami da fataucin muggan ƙwayoyi a jihar ta Bauchi.

Taron wanda uwargidan gwamnan jihar ta daukin nauyin gudanarwa tare da hadin gwiwar ma'aikatar jin dadin zamantakewa, matasa da kuma wasanni, ya wakana ne domin wayar da kan al'umma musamman matasa dangane da illoli na ta'ammali da miyagun ƙwayoyi.

Matar Gwamna Abubakar ta sha alwashin kawo ƙarshen ta'ammali da muggan ƙwayoyi a jihar Bauchi
Matar Gwamna Abubakar ta sha alwashin kawo ƙarshen ta'ammali da muggan ƙwayoyi a jihar Bauchi
Asali: Depositphotos

Hajiya Hadiza wadda uwargidan mataimakin gwamnan jihar ta wakilta, Hajiya Amina Katagum, ta bayyana damuwar ta dangane da yadda ta'ammali da muggan ƙwayoyi ke kara yaduwa a jihar.

KARANTA KUMA: Sanata Akpabio da Ministoci 9 na cikin tawagar Shugaba Buhari zuwa Kasar Sin

Kazalika uwargidan gwamnan ta bayyana cewa, akwai muhimmanci kwarai da aniyya ga dukkanin masu ruwa da tsaki akan su hada kai wajen yakar wannan annoba ta miyagun ƙwayoyi dake gurbata rayuwar da kuma makomar matasa a jihar.

Ta kara da cewa, wannan taro zai zamto a tashi a farga ga matasa dangane da hadurra dake tattare da ta'ammali na miyagun miyagun ƙwayoyi tare da karfafa gwiwar su wajen kauracewa zaman kashe wando.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel