Kotu ta hana mikawa Kwankwaso PDP a Kano

Kotu ta hana mikawa Kwankwaso PDP a Kano

- Wata babban kotu da ke jihar Kano ta umurci bayar da umurnin dakatar da rushe shugabanin jam'iyyar na jihar Kano

- Wannan umurnin ya daure hannun hedkwatan jam'iyyar da ke Abuja da shugaban jam'iyyar, Uche Secondus, daga yin katsalandan cikin tsarin jam'iyyar na Kano

- Wasu masu fashin baki a siyasa sun ce Sanata Kwankwaso ne ke kawo canji a shugabancin jam'iyyar domin ya daura mabiyansa

Wata babban kotu da ke jihar Kano ta hana hedkwatan jam'iyyar PDP na kasa da Ciyaman din jam'iyyar, Uche Secondus, rushe shugabancin jam'iyyar karkashin Ciyaman din jihar Masaud Jibrin El-Doguwa.

A yayin da yake gargadi a kan lamarin, Alkalin kotun, Justice N.S Umar ya ce kotun ta umurci wadanda suka shigar da kara da wadanda a kai kararsu da kada su aikata wani abu da zai canja tsarin jam'iyyar har zai kotun ta zartas da hukunci kan dambarwar da ake a jihar.

Shekarau: Kotu ta hana mikawa Kwankwaso PDP a Kano
Shekarau: Kotu ta hana mikawa Kwankwaso PDP a Kano
Asali: Depositphotos

Kazalika, Alkalin ya yi gargadin cewa kotu ta hana wani mahaluki ko mutane daga yin katsalandan kan wa'addin mulkin shugabanin jam'iyyar masu ci a yanzu.

DUBA WANNAN: A karo na farko bayan tsige shi, Lawal Daura ya yi magana kan mamaye majalisa

Alkalin ya kara da cewa, a madadin Sanata Jibrin El-Doguwa da jam'iyyar PDP, kotu ta hana uwar jam'iyyar daga yin wata yunkurin na sauyi cikin tsarin jam'iyyar na jihar, kananan hukumomi da gundumomi kamar yadda sashi na 47(1) da 223(1) (a) na kudin tsarin mulki na 1999 ya basu kariya.

Alkalin kotu ya daga cigaba da sharia'r zuwa ranar 5 ga watan Nuwamban 2015 domin zartar da hukunci.

Majiyar Legit.ng ta tattaro cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ke yunkurin sauya shugabancin jam'iyyar ta yadda zai samu ikon mallakar 65% na jam'iyyar domin ya zama shine zai rika juya jam'iyyar sai dai tsohon gwamna Shekarau bai amince ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel