Balarabe Musa ya sauka daga matsayin shugaban jam’iyyar PRP

Balarabe Musa ya sauka daga matsayin shugaban jam’iyyar PRP

- Shugaban jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP) , Balarabe Musa yace zai yi murabus daga kujerarsa na shugabancin jam'iyyar

- Musa yace hakan ya biyo bayan yawan shekarunsa, lafiyarsa da ya zoma ja da kuma bukatar ba matasa dama

- Yayi godiya ga mambobin jam'iyyar kan gudunmawar da suka bashi a lokacin da yake jagorantarsu

Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma shugaban jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) na kasa, Alhaji Balarabe Musa ya bayyana cewa zai sauka daga matsayin shugaban jam’iyyar, a jiya Alhamis, 30 ga watan Agusta.

Musa yace ya yi wannan yunkuri domin akwai bukatar yin hakan saboda girma ya zo masa, sannan lafiyar jikinsa ya fara ja da kuma bukatar barin matasa su gudanar da lamuran jam’iyyar.

Balarabe Musa ya sauka daga matsayin shugaban jam’iyyar PRP
Balarabe Musa ya sauka daga matsayin shugaban jam’iyyar PRP
Asali: Depositphotos

Ya bayyana hakan ne yayinda ya kaddamar da taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar karo na 54 a jiya.

Dattijon ya kuma bayyana cewa zai cigaba da kasancewa a jam’iyyar PRP.

KU KARANTA KUMA: Jami’ar sojojin Najeriya zai fara aiki kafin karshen 2018 - Buratai

Ya kuma bayyana cewa wanda zai gaje shi zai zamo matashi kuma mutum mai jajircewa akan tafarkin da jam’iyyarsu ta PRP ke kai.

Yayi godiya ga mambobin jam’iyyar maza ta mata kan irin goyon bayan da suka basa tsawon shekarun da yayi yana jagorantarsu cewa su bayar da irin wannan gudunmawa ga magajin shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel