APC za ta yi amfani da shirin zaben fidda dan takara na duk dan jam’iyya a zaben shugaban kasa kadai

APC za ta yi amfani da shirin zaben fidda dan takara na duk dan jam’iyya a zaben shugaban kasa kadai

Kwamitin Koli na Jam’iyyar APC ta yarda da yin amfani da shirin zaben fidda dan takarar shugaban kasa ne kadai ta hanyar shirin zaben fidda gwani na duk mai mallakin katin jam’iyya wato (Direct).

Hakan ya biyo bayan sakamakon ganawa da kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta a yau a babban sakatariyar jam’iyyar dake birnin tarayya Abuja.

Legit.ng ta tattaro cewa bayan dogon tattaunawa da muhawara, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yanke shawaran amfani da tsarin kullaliyar zaben fidda gwani a dukkanin kujerun takara sabanin kujeran shugaban kasa.

APC za ta yi amfani da shirin zaben fidda dan takara na duk dan jam’iyya a zaben shugaban kasa kadai
APC za ta yi amfani da shirin zaben fidda dan takara na duk dan jam’iyya a zaben shugaban kasa kadai
Asali: Twitter

Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya bayyanawa manema labarai cewa jihohi zasu iya zaben buddadiyar zaben fidda gwani idan bukatan haka ya zo.

KU KARANTA KUMA: Idan har siyasar ka don mutane ne toh ku rungumi zaben fidda gwani – Shehu Sani

A baya Legit.ng ta rahoto cewa an samu gagarumin rabuwar kai a jam’iyya mai mulki ta All Progressives Party (APC) kan sabuwar tsarin gudanar da zaben fidda gwani da jam’iyyar ke shirin amfani da shi gabanin zaben 2019.

Majiya a jamiyyar sun bayyanawa jaridar Daily Trust cewa a jiya, yawancin yan jam’iyyar musamman gwamnoni sun nuna rashin yardarsu da bari mambobin jam’iyya gaba daya su kada kuri’a wajen zaben fidda gwani.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel