Guguwar sauyin sheƙa ba ta gurgunta jam'iyyar APC ba - Buhari

Guguwar sauyin sheƙa ba ta gurgunta jam'iyyar APC ba - Buhari

Rahotanni da sanadin shafin jaridar The Nation sun bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi furuci dangane da ficewar wasu jiga-jigan mambobi na jam'iyyar APC inda suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Ko shakka babu makonni kadan da suka gabata ne wasu kusoshin jam'iyyar APC da suka hadar da shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, gwamnonin jihar Kwara, Sakkwato da Benuwe da kuma wasu mambobi na majalisar dokoki ta tarayya suka yi hannun riga da jamm'iyyar.

Sai dai a yayin da shugaba Buhari ke ganin jiga-jigan da suka raba gari da jam'iyyar sun aikata hakan ne domin gurgunta jam'iyyar ba su cimma nasarar da suka kudirta ba, inda ya ce ba bu wata illa da ficewar su ta haifar face karuwar inganci.

Guguwar sauyin sheƙa ba ta gurgunta jam'iyyar APC ba - Buhari
Guguwar sauyin sheƙa ba ta gurgunta jam'iyyar APC ba - Buhari
Asali: Facebook

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yayin taron kusoshin jam'iyyar karo na shida da aka gudanar cikin babban birnin kasar nan na tarayya a ranar yau ta Alhamis.

KARANTA KUMA: Attajirai 15 za su dauki nauyin Takarar Bianca Ojukwu

A yayin haka kuma shugaban jam'iyyar na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa ba bu abinda ficewar wasu daga cikin kusoshin jam'iyyar ta haifar face kara mata kaimi gami da karfafuwar ta kan akidar kawo sauyi a kasar nan.

Shugaban kasar wanda ya isa harabar taron da misalin karfe 11.20 na safiyar yau, ya kuma ja hankali tare da bayar da tabbacin sa na aiwatar da gaskiya da kuma adalci yayin gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyyar da kuma babban zabe na 2019.

Kazalika shugaban kasar ya kara da cewa, guguwar sauyin sheƙar ba ta haifar da komai ba sabanin yadda kusoshin jam'iyyar suka ƙudirta domin kuwa haƙar su ba ta cimma ruwa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel