Sabon bincike: Awaki na iya banbance mutane masu fushi da masu fara'a

Sabon bincike: Awaki na iya banbance mutane masu fushi da masu fara'a

- Sabon bincike daga kasar turai ya nuna cewa Awaki na iya gane mutane masu fushi da masu farin ciki

- Masana kimiyar da suka gudanar da wannan bincike, sun yi amfani da Awaki 35

- Tuni dama masana kimiya suka gano cewa dabbobi kamarsu Karnuka da Dokuna, na iya musayar zance tsakaninsu da mutane

Wani sabon bincike ya nuna cewa Awaki sunfi son zama a kusa da mutane masu fara’a a fuskarsu, mai maikon wadanda kullum suke a cikin fushi, wanda hakan ya nuna cewa irin wannan dabi’a tafi yaduwa a tsakanin dabobbi, sabanin yadda bincike ya nuna akasin hakan a baya.

Binciken, wanda wasu kwararrun masana kimiya daga kungiyar “British Royal Society” suka gabatar don gano irin baiwar da Awaki ke tattare da ita na karantar halayen dan Adam, sun yi amfani da Awaki 35 don gudanar da wannan bincike.

Masu binciken sun rinka nunawa Awakan hotunan mutane daban daban, wasu cikin fara’a, wasu kuma cikin fushi.

Sakamakon binciken ya nuna cewa Awakan sunfi nuna sha’awarsu ga mutanen dake cikin fara’a, da kuma nuna son dadewa suna kallon hotunan, yayin da suke gaza daukar dogon lokaci kusa da hotunan mutanen dake cikin fushi.

KARANTA WANNAN: Hukumar INEC tasha alwashin gurfanar da duk wanda ta samu da laifin siyen kuri'u

Daga karshe masu binciken, sun yanke hukunci cewa: “Awaki zasu iya banbance fuskar da ta ke cikin fara’a da wacce ta ke cikin bacin rai, wanda hakan ke nuni da cewa zasu iya banbance yanayin da ‘dan Adam yake ciki”

Tuni dai dama masana kimiya suka gano cewa Karkuna da Dokuna na iya fahimtar zance tsakaninsu da mutane, inda suka yi amanna da cewa hakan ya faru ne sakamakon samun matsugunni da sukayi a cikin jama’a, da zamtowa kamar abokan rayuwa.

Sai dai wannan sabon bincike shine na farko da ya nuna cewa dabbobi kamar Awakai, wadanda ba’a basu wata muhimmiyar damar cudanya da mutane ba, zasu iya fahimtar yanayin da ‘dan Adam yake ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel