Fusatattun matasa a Legas sun yi fito na fito da jami’an Yansanda, sun kashe Dansanda

Fusatattun matasa a Legas sun yi fito na fito da jami’an Yansanda, sun kashe Dansanda

Babu sididi babu sadada, hakanan siddan wasu gungun matasa bata gari sun kai ma wata karamar rundunar Yansanda hari akan titin College dake yankin Ifako Ijaiye na jihar Legas, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yayin wannan hari da fusatattun matasan suka kai sun kashe jami’in Dansanda guda daya tare da jikkata guda uku, sa’annan suka banka ma motar Yansandan wuta.

KU KARANTA: Rayukan mutane 8 da gidaje 95 sun salwanta a wani hari da aka kai jahar Filato

Sai dai kaakakin rundunar Yansandan jahar, Chike Oti ya bayyana cewa sun kama mutane biyar dake da hannu cikin harin da aka kai ma jami’ansu, wanda yace a yanzu haka suna garkame a babban ofishin Yansanda dake kula da manyan laifuka.

Kaakaki Oti ya sanar da haka ne a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba, inda yake tabbatar da faruwar lamarin, kamar haka:

“Da misalin karfe 11 na safiyar Talata, 28 ga watan Agusta akan titin college dake Ifajo ijaiye a jihar Legas, wasu gungun matasa sun kai ma Yansanda hari yayin da suke bakin aiki.wanda

“Har yanzu bamu san dalilin wannan hari ba, amma a dalilin wannan hari, mun rasa jami’in Dansanda guda daya mai suna Sajan Esiabor Collins, sa’annan sun kona motar aiki guda daya.” Inji Chike.

Binciken farko farko da hukumar Yansanda ta gudanar ya nuna cewa da fari matasan sun fara zuwa ofishin Yansanda na ‘Area G’ dake Ogba da nufin su kai hari sakamakon mutuwar wani matashin unguwar kimanin makonni biyu bayan yayi fada da Dansanda, amma sai suka fahimci hakan ba zai yiwu ba.

“Duk da cewa hukumar Yansanda bata da wata masaniya game da hakan, amma kwamandan Yansandan ofishin ya basu hakuri, inda ya tabbatar musu zasu gudanar da bincike game da lamarin, daga nan ne suka nufi motar Yansanda suka kai musu hari.” Inji shi.

A nasa jawabin, kwamishinan Yansandan jihar, Edgal Imohimi ya nuna bacin ransa da yadda wasu mutane ke daukar doka a hannunsu, ta yadda suke da karfin zuciyar kashe Yansanda ba cas ba as, don haka yace Yansanda zasu fara amfani da makamai wajen kare kansu daga irin wadannan matasa, ko kuma idan suka kamasu suna kokarin kashe wani ko lalata kayan gwamnati.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel