Dukkan mai rai mamaci ne: Yadda wani Alhajin Najeriya ya gamu da ajalinsa a Makka

Dukkan mai rai mamaci ne: Yadda wani Alhajin Najeriya ya gamu da ajalinsa a Makka

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, wani mahajjaci daga Najeriya ya rasu a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta a birnin Makkah sakamakon wani mummunan tsautsayi daya fada masa, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Laraba 29 ga watan Agusta, a lokacin da mahajjacin ya fada cikin ramin da na’urar dake daukan tare da sauko da mutane daga gidajen sama mai tsawo (Lifter).

KU KARANTA: Sunnah leka gidan kowa: kungiyar Izala ta bude ofis a birnin Makkah

Rahotanni sun bayyana cewa mahajjacin ya shiga cikin na’urar ne da nufin yayi amfani da shi, sai dai abinda da rashin sani, wanda bahaushe yace yafi dare duhu, ashe ana gyaran na’aurar ne, daga nan sai kawai ya zurma, sai gawarsa kawai aka tsinta.

Sai dai nan da nan hukumar kula da alhazan Najeriya ta tattaro jami’an hukumar kwana kwana suka isa inda abin ya faru, inda suka dauko gawartasa, wanda hukumar ta bayyana shi a matsayin mahajjaci daga jahar Neja.

Daga karshe shugaban kwamitin likitocin Najeriya Dakta Ibrahim Kana yace ana cigaba da duba bidiyon hatsarin don samun cikakken bayani. mutuwar wannan mutumi ya kawo adadin mahajjatan Najeriya da suka rasu a kasa mai tsarki zuwa mutum bakwai.

A ranar Litinin din data gabata ne rukunin mahajjata na farko daga jahar Sakkwato suka fara dawowa gida Najeriya daga kasar Saudiyya, zuwa yanzu mahajjata da dama daga jihohi daban daban sun dawo gida.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel