Naira dubu 900: Wani babban malamin Izala ya cinye kudin masallaci a Kano

Naira dubu 900: Wani babban malamin Izala ya cinye kudin masallaci a Kano

- Wani babban malamin Izala ya cinye kudin masallaci a Kano

- Naira dubu 900 ne ya cinye

- Anyi anyi ya biya yaki biya

Babban Limamin masallacin Juma'a na unguwar Tudun Murtala dake a garin Kano, Sheikh Abdullahi Sale Pakistan ya hadu da fushin hukuma bayan da wata babbar kotun jihar ta umurci ya mayar da wasu kudaden da ya ansa na masallacin da ya karba.

Naira dubu 900: Wani babban malamin Izala ya cinye kudin masallaci a Kano
Naira dubu 900: Wani babban malamin Izala ya cinye kudin masallaci a Kano
Asali: Facebook

KU KARANTA: Naira dubu 100: Wata kabila a Arewa ta takaita kudin sadaki da Aure

Kudin dai kamar yadda muka samu sun kai adadin Naira dubu dari tara sannan kuma ya karbe su ne da sunan bashi kusan shekaru biyu kenan da suka gabata.

Legit.ng ta samu cewa Alkalan babbar kotun jihar Masu Shari'a Patricia A. B. Mahmoud da kuma Abdullah Mahmoud Bayero sune suka yanke hukuncin bayan sun yi fatali da hukuncin da wata karamar kotu a jihar ta yanke akan lamarin.

Haka zalika mun samu cewa tun farko dai kudin da aka tara suna a hannun kwamitin amintattu ne na gidauniyar ida kammala ginin masallacin tunawa da Sheikh Jafar a unguwar Sabuwar Gandu da ke a karamar hukumar Kumbotso.

A wani labarin kuma, Kamar dai kasashe da dama a nahiyar Afrika, lamarin nan na tabe dake tattare da halayyar luwadi da madigo na cigaba da fuskantar kyama daga al'umma da ma hukumomin gwamnatoci a kowane mataki a tarayyar Najeriya.

Sai dai hakan na nema ya fara sauyawa bayan da wani dan takarar shugaban kasa a tutar jam'iyyar adawa ta PDP kuma tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas, Donald Duke ya bayyana cewa shi zai sakar masu mara suyi fitsari idan har ya zama shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel