Sunnah leka gidan kowa: kungiyar Izala ta bude ofis a birnin Makkah

Sunnah leka gidan kowa: kungiyar Izala ta bude ofis a birnin Makkah

Shuwagabannin kungiyar Izalatil bidi’a wa iqamatissunnah a karkashin shugaba Sheikh Bala Lau sun halarci taron bude sabon katafaren ofishin kungiyar a bikin Makkah dake kasar Saudiyya, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Gwamnatin kasar Saudiyya ta baiwa kungiyar Izala damar bude wannan ofishi ne a unguwar Khakiya dake cikin birnin Makkah don cigaba da aikin watsa Kalmar Allah ta hanyar gudanar da Da’awa.

KU KARANTA: Takarar shugaban kasa: Kwankwaso yayi zargin gwamnatin tarayya na masa bita da kulli

Sunnah leka gidan kowa: kungiyar Izala ta bude ofis a birnin Makkah
Bala Lau
Asali: Original

Shugaban kungiyar, Sheikh Bala Lau yace musabbabin bude wannan ofis shine don ciyar da harkokin wa’azi da kungiyar ta kafo akai, kuma ta kwashe tsawon shekara da shekaru tana yadawa.

“Don haka wannan ofis zai hada kasashen Duniya dake da alaka da alhulussunnah, ta yadda za’a dinga haduwa ana tattauna batutuwan da suka shafi da’awar Sunnah a kasashen.” Inji sheikh Bala Lau.’

Sunnah leka gidan kowa: kungiyar Izala ta bude ofis a birnin Makkah
Ofishin
Asali: Facebook

Bugu da kari Sheikh Bala Lau yace ofishin zai zama wata cibiya da zata dinga shirya wa’zuzzuka da nasihohi a unguwanni, lunguna da sako sakon dake cikin garin Makkah don karantar da jama’an Najeriya dake yankunan, tare da taimaka ma alhazan Najeriya.

Daga cikin malaman da suka halarci taron bude ofishin akwai Malam Yakubu Musa, Malam Kabir Gombe, Malam Abubakar Giro Argungu, Malam Mustapha Imam Sitti, Dakta Ibrahim Rijin Lemo, Malam Umar Jega, Abdulkadir Kazaure.

Sauran sun hada da shugaban Izala a jihar Kebbi, Isa Aliyu Jaen, Alaramma Isma’il Maiduguri, Ashiru Babandede, da sauran shuwagabannin kungiyar a matakin jaha jaha, yan agaji da sauran jama’a.

Sunnah leka gidan kowa: kungiyar Izala ta bude ofis a birnin Makkah
Taron
Asali: Facebook

A wani laabrin kuma, gwamnatin kasar Saudiyya ta baiwa kungiyar Izala lasisin gabatar da wa’azi da nasihohi a cikin garin Makkah don taimaka mata wajen ilimantar da jama’a akan koyarwar littafin Allah da hadisan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel