Kwankwaso: Shugaban Kasa Buhari na kokarin takurawa ‘Yan adawa – CUPP

Kwankwaso: Shugaban Kasa Buhari na kokarin takurawa ‘Yan adawa – CUPP

Hadakar Jam’iyyu na CUPP sun fito sun yi magana bayan an hana Sanata Rabiu Kwankwaso farfajiyar Eagles Square inda ya shirya kaddamar da shirin tsayawar sa takarar Shugaban kasa a Jam'iyyar PDP.

Kwankwaso: Shugaban Kasa Buhari na kokarin takurawa ‘Yan adawa – CUPP
CUPP yace Shugaban Kasa Buhari na jin tsoron Kwankwaso
Asali: Twitter

CUPP tayi kaca-kaca da Gwamnatin Tarayya da kuma Jam’iyyar APC na hana Rabiu Musa Kwankwaso filin da ya shirya kaddamar da bikin tsayawa takarar Shugaban kasa inda tace Gwamnatin Buhari ta na tsoron farin jinin irin su Rabiu Kwankwaso.

Jaridar Vanguards ta rahoto CUPP tana cewa Gwamnatin Buhari ta kama hanyar kama-karya da gigin mulki. Ikenga Ugochinyere, wanda shi ne ke magana da yawun Kungiyar adawar yace Buhari na kokarin hana ‘Yan adawa sakat a Najeriya.

KU KARANTA: Abin da ya sa na ke neman tsayawa takarar Shugaban kasa

Kungiyar hadakar ‘Yan siyasar tace ba yau aka saba yi wa Kwankwaso irin wannan wulakanci ba. A baya dai an kitsa da ‘Yan sanda an hana sa shiga Jihar sa ta Kano. Wannan ya sa CUPP ke kira Jama’a su guji zaben Shugaba Buhari a 2019.

Ana zargin Gwamnatin Najeriyar da amfani da ‘Yan Sanda da Jami’an tsaro wajen ganin bayan ‘Yan siyasar adawa. A jiya ne Gwamnati ta sanar da tsohon Gwamna Kwankwaso cewa ba za a ba sa dama yayi taro yau ba duk da an gama kammala shiri.

Jiya ne babbar Jam'iyyar adawa ta PDP tace za tayi bakin kokarin ta wajen ganin babban Kotun Duniya watau ICC ta kama Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda keta hakkin Bil Adama da cin zarafin al’ummar kasar da matsawa 'Yan adawa lamba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel