Yan sanda sun kama wasu ma’aurata masu tabin hankali dauke da sassan jikin dan Adam a Lagas

Yan sanda sun kama wasu ma’aurata masu tabin hankali dauke da sassan jikin dan Adam a Lagas

Jami’an yan sanda na Ijanikin dake jihar Lagas sun kama wasu ma’aurata dake karyan hauka dauke da sassan jikin dan Adam daban-daban sannan suna zama ne a karkashin gadar Cele tashar NICA, Ojo kan babban titin Mile 2 zuwa Badagary.

Lamarin ya haifar da rudani yayinda mazauna yankin suka kai farmaki wajen domin kama ma’auratan da suka ce karyan hauka suke yi.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ma’auratan na karyan hauka ne domin sun dauke hankalin mutane daga sanin cewa suna sana’an sassan jikin dan Adam ne.

Daya daga cikin mazauna yankin, Shade Oluwakemi ta bayyana cewa an fara kama matar ne. Tace ya dauki tawagar yan sandan da wasu mazauna yankin sa’o’i da dama kafin su iya janye mutumin, sanye da tufafi masu dauda daga karkashin gadar.

Yan sanda sun kama wasu ma’aurata masu tabbin hankali dauke da sassan jikin dan Adam a Lagas
Yan sanda sun kama wasu ma’aurata masu tabbin hankali dauke da sassan jikin dan Adam a Lagas
Asali: Facebook

Ta bayyana cewa ba don zuwan yan sandan ba, mazauna yankin sun shirya sanyawa ma’auratan wuta.

A cewar mazauna yankin matar ta kwashe watanni da dama tana zama a karkashin gadar.

Don haka mazauna yankin ke ta lura da duk wani motsi nasa har sai da aka gano wannan mumunan aiki nata a ranar Litinin.

Wata mazauna yankin, Arewa Sunday ta bayyana cewa an kama ta dauke da kawunan mutane uku da sassan jiki daban-daban a hannunta.

Idanun shaida ta bayyana cewa matar ta jefar da wayarta a cikin daji yayinda ta hangi jami’an tsaron da aka kira.

KU KARANTA KUMA: Babu amfanin yin mahawara tsakaninmu – APC ta maida martani ga PDP

Wata kuma tace hankalin mazauna yankin ya koma kanta ne a lokacin da suka lura da manyan motocin dake zarya a wajen da take.

Wasu lokutan kuma sunce sukan ga hayaki na tashi daga inda take zama a karkashin gadar sai su dauka girki take yi ashe dai tana gasa sansan jikin mutane ne.

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Lagas, CSP Chike Oti ya tabbatar da lamarin yace suna kan ci gaba da bincike a yanzu haka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel