Toh fa! Hukumar Soji zata ladabtar da wasu Sojoji da suka tafka babban laifi a Maiduguri

Toh fa! Hukumar Soji zata ladabtar da wasu Sojoji da suka tafka babban laifi a Maiduguri

Hukumar rundunar Sojan kasa ta Najeriya ta dauki alwashin ladabtar da dukkanin Sojojin dake da hannu cikin wani bore da Sojoji suka yi a satin biyu da suka gabata a filin sauka da tashin jiragen sama dake garin Maduguri, kamar yadda dokokin hukumar suka tanadar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sojojin sun yi wannan bore ne don nuna rashin amincewarsu da sake tura su wasu garuruwan jihar Borno don yaki da Boko Haram, yayinda su kuma suke ganin lokaci yayi daya kamata su koma gida sakamakon sun kwashe tsawon shekaru da dama a jihar Borno.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya ambaci mutane 4 da ba zai taɓa ɗaga musu ƙafa ba har abada

Dayake jawabi a yayin wani taro, babban kwamandan Sojojin dake yaki da yan Boko Haram, Kwamanda A.A Dikko ya bayyana cewa akwai tsarin ladabtarwa dake tattare da yin bore a aikin Soja, don haka dole ne Sojojin su dandana kudarsu.

“Bama horas da Sojoji, muna ladabtar dasu ne, ladabi shine ginshikin aikin Soja, idan har babu ladabi, toh babu rundunar Sojan kasa, don haka duk Sojan daya kauce hanya, sai an dawo masa da saiti.

“Duk wanda ya shiga aikin Soja, tabbas ya yanke shawarar sadaukar da rayuwarsa don kare iyakokin Najeriya, don haka yake da muhimmanci da mu tuna ma Sojoji aikinsu da kuma rawar da ya kamata su taka.” Inji shi.

Daga karseh Kwamanda Dikko yayi kira ga Sojoji da su kasance masu ladabi, inda yace dole ne Soja ya kasance cikin ladabi a koyaushe, kuma dole ne Soja ya kasance cikin shirin bin umarnin na gaba da shi a kullum.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel