Bolaji Abdullahi ya bayyana kudirinsa na takarar kujerar gwamnan Kwara

Bolaji Abdullahi ya bayyana kudirinsa na takarar kujerar gwamnan Kwara

- Tsohon kakakin jam'iyyar APC ya kaddamar da kudirinsa na son takarar kujerar gwamna a jihar Kwara

- Bolaji Abdullahi ya ayyana kudirinsa ne a lokacin bikin babban Sallah

- Yayi alkawarin kawo ci gaba da hadin kai a tsakanin mutanen jihar wadda ya rabu gida biyu

Bolaji Abdullahi, tsohon kakakin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayyana kudirinsa na son takarar kujerar gwamna a jihar Kwara.

Abdullahi ya bayyana kudirinsa a lokacin da yan uwa da abokan arziki suka ziyarce shi a lokacin bikin Sallah a gidansa dake Ilorin, baban irnin jihar Kwara a ranar Alhamis.

Tsohon ministan yace yana neman zama gwamna ne domin kawo chanji a Kwara.

Bolaji Abdullahi ya bayyana kudirinsa na takarar kujerar gwamnan Kwara
Bolaji Abdullahi ya bayyana kudirinsa na takarar kujerar gwamnan Kwara

Yace abun kaico ne cewa an raba kawunan matasa a jihar zuwa ga wadanda ke kin shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da wadanda ke son sa.

KU KARANTA KUMA: Ba zamu taba janye wa Ortom ba – Yan takarar PDP 12

Yace idan har aka zae sa a matsayin gwamna, zai yi aiki domin hada kan jama’a domin ci gaban jihar.

Idan dai dai bazaku manta ba Abdullahi yayi murabus a matsayin kakakin jam’iyyar APC a ranar 1 ga watan Agusta. Yace ya yi murabus ne saboda ana tantama akan biyayyarsa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa rikicin da ake fama dashi kan dakatar da sanatan dake wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani da kuma wanda zai samu tikitin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a wannan yankin na kara kamari.

Mataimakin sakataren shiri na jam’iyyar APC, Hon. Muhammad Sani Ibrahim a jiya ya kaddamar da cewa babu wani mutum da zai iya ba kowani mamba tikitin jam’iyyar kai tsaye.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel