Tawagar Najeriya ta tafi zuwa gasar wasan tebur na nakasassu a China

Tawagar Najeriya ta tafi zuwa gasar wasan tebur na nakasassu a China

- Tawagar 'yan wasan Nigeria masu buga wasan kwallon teburi ta masu nakasa sun tafi Beijing, kasar China

- Tawagar na dauke da 'yan wasa Hudu, mace daya da maza uku

- Mai kula da tawagar ya bada tabbacin cewa 'yan wasan sun samu kyakkyawan horo

A ranar lahadinan 26 ga watan Augusta, tawagar ‘yan wasan Nigeria masu nakasa da ke buga wasan kwallon teburi suka bar kasar Nigeria zuwa birnin Beijing da ke kasar Sin, don shiga gasar babban kofin kwallon teburi na duniya na masu nakasa mai taken “World Para Table Tennis Championship”

Tawagar wacce ta had’a da mace daya da maza uku, sun bar kasar ne a cikin jirgi mallakin kasar Ethopia.

Mace daya jal da ke a cikin tawagar mai suna Faith Obazuaye, na tare da abokan wasanta, Nasiru Bello, Tajudeen Agunbiade da kuma Olufemi Alabi.

Tawagar na karkashin kulawar Anderson Bankole, wanda ke kula da fannin shirin gasar kwallon teburin na masu nakasa a kasar, karkashin inuwar hukumar dake kula da wasan teburi ta Nigeria (NTTF).

KARANTA WANNAN: Fasinjoji na mutuwa saboda direbobi masu matsalar gani -FRSC

Har ila yau a cikin tawagar akwai Victor Anusa, tsohon sakataren hukumar ta NTTF. Tawagar ‘yan wasan zasu ci gaba da samun horo karkashin mai horas da wasan teburi, Sunday Odebode.

Za’a fara buga gasar cin kofin ne a ranar 27 ga watan Augusta, a kamala a ranar 3 ga watan Satumba.

Bankole wanda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na NAN a wayar taro gabanin tafiyar su cewa ‘yan wasan sun shirya don fuskantar wannan gasar, ya kuma ce sun samu kyakkyawan horo da zai iya sa su samu gagarumar nasara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel