Kisan wani dalibi ya jefa jami’in SARS cikin chakwakiya

Kisan wani dalibi ya jefa jami’in SARS cikin chakwakiya

- Kowa ya debo da zafi bakinsa in ji masu iya magana

- Wani jami'in tsaro ya sha tafi karfinsa bayan da ya bidige wani dalibi har lahira

- Tuni har an damke shi domin fara tuhumarsa

Jami'an tsaron rundunar ‘yan sanda na kasa reshen jihar Osun, sun damke wani dan sanda na musamman dake aiki da sashin yaki da masuaikata manyan laifuka (SARS) na ofishin ‘yan sanda na Iwo bisa laifin bindige wani dalibin kwalejin kimiyya da fasaha mai suna Tunde Nafi'u.

Kisan wani dalibi ya jefa jami’an SARS cikin chakwakiya
Kisan wani dalibi ya jefa jami’an SARS cikin chakwakiya

‘Dan sandan na SARS ya bindigen dalibin ne mai kimanin shekaru 30 a duniya a unguwar Agboigboro a yankin Iwo, wanda hakan ya haifar da zanga-zanga a tsakanin matasa, har sai da takai ga kone ofishin ‘yan sanda na Iwo.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Osun Mista Fimihan Adeoye ya bayyanawa manema labarai cewa an kame wannan dan sandan ne tare da tsare shi a babban birnin jihar wato Osobgbo.

KU KARANTA: ‘Yan bingida sun hallaka mutane 2 ciki har da direban kakakin majalisar Filato

Ya kara da cewa rundunar ‘yan sanda ta kaiwa ziyara ga iyalin wanda aka kashe din, tare kuma da bayar da tabbacin ganin shari'a ta yi aikinta akan wanda ya aikata laifin.

A karshe kakakin rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar ta Osun Folasade Odoro ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da damke mutune 31 bisa laifin barnata dukiya da kuma lalata motar jami'an yan sanda.

"Sun kone gidaje tare da ofisoshi da motocin ‘yan sandan guda 3 da wadansu guda 2 mallakin babban mukaddashin baturen ‘yan sandan jihar".

"Kawo yanzu dai an samu kwanciyar hankali tare da cigaban al'amuran kasuwanci a yankin, kamar yadda aka saba"

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel