2019: Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayar da ta dauka a kan fitar da dan takara

2019: Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayar da ta dauka a kan fitar da dan takara

A yayin da zabukan shekarar 2019 ke kara matsowa, babbar jam'iyyar adawa, PDP, ta bayyana cewar ba ta cikin maganganun da ake yadawa a gari cewar zata tsayar da dan takarar shugaban kasa ne ta hanyar sulhu.

Jam'iyyar ta bayyana cewar babu maganar batun yin sulhu tsakanin masu neman jam'iyyar ta tsayar da su takarar shugaban kasa tare da bayyana cewar ta fi mayar da hankali a kan yadda zata tabbatar da adalci da bawa dukkan 'yan takarar damar gwada sa'ar su.

Wasu masu ruwa da tsaki a cikin PDP na nuna damuwar su bisa yawaitar 'yan takarar dake neman jam'iyyar ta tsayar da su takara a zaben 2019.

A yanzu haka akwai ‘yan takarar shugaban kasa mutum 11 a jam’iyyar ta PDP. Sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, gwamnan jihar Kano, Aminu Waziri Tambuwal, gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na jihar Gombe, tsohon ministan harkoki na musamman, Tanimu Turaki da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi.

2019: Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayar da ta dauka a kan fitar da dan takara
Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayar da ta dauka a kan fitar da dan takarar shugaban kasa

Akwai tsoffin gwamnonin jihar Kano, Ibrahim Shekarau da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, takwaransa na jihar Jigawa, Sule Lamido, da kuma dan gwagwarmaya Dakta Baba Datti Ahmed.

DUBA WANNAN: Gwamnonin PDP sun juyawa daya daga cikinsu baya

Tuni wasu masu ruwa da tsaki a PDP din ke matsin lamba ga shugaban jam'iyyar, Uche Secondus, a kan ya nemo hanyar da za a bi domin a rage yawan 'yan takarar da jam'iyyar ke da su.

Sai dai sakataren watsa labarai na PDP, Kola Ologbodian, ya shaidawa manema labarai a jiya, Asabar, cewar jam'iyyar ba ta da niyyar kokarin rage 'yan takarar da take da su ko neman wani ya janye takarar sa matukar ba 'yan takarar ne da kansu suka yanke shawarar fitar da daya daga cikinsu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel