2019: Abin da za a batar kan abinci ba zai wuce Biliyan 1 ba - INEC

2019: Abin da za a batar kan abinci ba zai wuce Biliyan 1 ba - INEC

Mun samu labari cewa kwanaki Hukumar zabe na kasa watau INEC ta karyata maganar cewa ta ware makudan kudi har Naira Biliyan 6 domin ciyar da ‘Yan Sandan Kasar nan a zabe mai zuwa na 2019.

2019: Abin da za a batar kan abinci ba zai wuce Biliyan 1 ba - INEC
INEC ta karyata rade-radin shirin kashe Biliyan 6 a kan harkar abinci

Hukumar ta INEC tace ta ware kudin da za ta ciyar da dukkanin Ma’aikata da Malaman zabe ne ba wai ‘Yan Sanda kurum ba. INEC a wani karin haske da tayi tace wadanda za a ciyar sun hada da ‘Yan Sanda, da ma Ma’aikatan gidan yari.

Hukumar zaben ta kuma tabbatar da cewa sauran wadanda za a dauki nauyin ba abinci sun hada da Jami’an tsaro na NDLEA da Ma’aikatan da ke lura da shige da fice cikin kasar nan. INEC ta ce kudin da aka ware din bai kai Biliyan 6 ba.

KU KARANTA: Gwamnonin PDP sun juyawa daya daga cikin su baya

INEC tayi wannan bayani ne ta shafin Facebook kwanan nan inda ta bayyana cewa za kuma ta dauki nauyin ciyar da Malaman zabe wadanda su ka hada da masu lura da akwati da masu sanar da sakamako da masu tara kuri’un zaben.

Ko da dai Hukumar ta INEC ba ta bayyana abin da za ta kashe wajen ciyar da masu aiki a ranar zaben ba, Hukumar ta nuna cewa ainihin abin da aka ware bai kai kashi 25% na kudin da ake fada ba. Akalla dai kenan INEC ta batar da Biliyan guda.

Ana dai sa rai Majalisa ta amince da kasafin kudin Hukumar zaben wanda ya kusa kai Naira Biliyan 250. Daga cikin wannan kudi za ayi amfani Miliyoyi wajen ciyar da karnuka har da dawakai a zaben mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel