2019: Dan takarar PDP ya yi tsokaci kan farin jini Buhari a arewa

2019: Dan takarar PDP ya yi tsokaci kan farin jini Buhari a arewa

- Sanata Ahmed Makarfi ya gargadi jam'iyyarsa na PDP game da farin jinin da Buhari ke dashi a arewa

- Makarfi ya ce jam'iyyar PDP na bukatar dan takara wanda jama'a za su amince dashi muddin suna son lashe zaben 2019

- Tsohon gwamnan jihar Kadunan, ya bayyana bangarorin da zai mayar da hankali idan ya lashe zaben

Dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Sanata Ahmed Makarfi ya gargadi jam'iyyarsa ta PDP cewa dole su tsayar da dan takara mai nagarta da farin jini muddin suna son kayar da shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

The Nation ta ruwaito cewa Makarfi ya gargadi masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP cewa har yanzu shugaba Muhammadu Buhari yana da farin jini sosai a yankin arewa kuma yankin ne tafi sauran yawan masu kada kuri'a.

Makarfi ya bayyana abu daya da PDP za tayi muddin tana son kada Buhari a 2019
Makarfi ya bayyana abu daya da PDP za tayi muddin tana son kada Buhari a 2019

Makarfi wanda tsohon Ciyaman din rikon kwarya na PDP ne ya ce ya zama dole jam'iyyar PDP ta yi kokarin sauya tunanin masu zabe a yankin arewa saboda har yanzu mafi yawancinsu 'yan a mutun shugaba Muhammadu Buhari ne.

DUBA WANNAN: Hukumar 'yan sanda ta gayyaci Fani Kayode saboda kalaman kin addini

Rahoton ya ce Makarfi ya yi wannan maganar ne a ranar Juma'a yayin wata taro da ya yi deleget din jam'iyyar PDP na jihar Ekiti karkashin jagorancin mataimakin gwamna, Farfesa Kolapo Olusola a kokarinsa na kamfen din samun tikitin takarar shugabacin kasa gabanin taron jam'iyyar.

Makarfi ya yi alkwarin zai magance matsalar rashin tsaro, rashin ayyukan yi, matsalar wutan lantarki da sauran matsalolin da ke adabar Najeriya muddin aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

"idan muna son muyi nasara a zaben 2019, kar mu sake mu rasa kuri'un mutanen arewa kuma dole mu dan takarar da zasu amince dashi.

"Matsalar mu shine lashe zabe a arewa, shugaban kasa mai ci yanzu dan arewa ne kuma jama'a sun matukar kaunarsa. Idan muna son muyi nasara sai mu fitar da dan takara daga arewa.

"Dole mu yi kokarin sauya tunanin 'yan gani kashe nin Buhari domin su karkato zuwa gare mu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel