Ficewar Tsohon Gwamna, Uduaghan, ta girgiza jam'iyyar PDP, APC ta dara

Ficewar Tsohon Gwamna, Uduaghan, ta girgiza jam'iyyar PDP, APC ta dara

Watsi gami da ficewa daga jam'iyyar PDP ta wani tsohon gwamnan jihar Delta, Dakta Emmanuel Uduaghan, ta zamto tamkar wata girgiza ga jam'iyyar da kuma jiga-jiganta na jihar, sai dai wannan rahoto mai dadawa ne ga jam'iyyar APC.

A yayin da jam'iyyar APC ke murna gami da madalla dangane da wanna lamari, tana kuma zawarcin tsohon gwamnan inda aka bar jam'iyyar PDP cike da mamaki na wannan babban rashi da ta yi a jihar ta Delta.

Gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa, tare da wasu shugabannin jam'iyyar na jihar, sun tattauna dangane da wannan lamari na bazata, inda suke yunkurin gindaya dabaru da zu dakile jam'iyyar APC ta mallake jihar.

Legit.ng ta fahimci cewa, jiga-jigan jam'iyyar na wannan fargaba ta mamayar jam'iyyar APC a jihar wanda tun a baya shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshimhole, ya jaddada ma su yiwuwar hakan.

Ficewar Tsohon Gwamna, Uduaghan, ta girgiza jam'iyyar PDP, APC ta dara
Ficewar Tsohon Gwamna, Uduaghan, ta girgiza jam'iyyar PDP, APC ta dara

Wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar na jihar sun bayyana mamakin su yayin ganawa da manema labarai dangane da ficewar tsohon gwamnan jihar.

KARANTA KUMA: Sai mun girgiza Buhari da jam'iyyar APC - Secondus

Jiga-jigan jam'iyyar sun bayyana cewa, akwai mamaki dangane da yadda gwamnan jihar Sanata Okowa ya zuba idanu kan warwarewar alakar sa da tsohon gwamnan da ya ci gajiyar kujerar sa a karkashin jam'iyyar a zaben 2015.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jam'iyyar PDP ta kuma rasa mambobinta kimanin 5000 da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a can jihar Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel