Shugaba Buhari ya nufi Abuja bayan kammala hutun sa na Sallah a garin Daura

Shugaba Buhari ya nufi Abuja bayan kammala hutun sa na Sallah a garin Daura

A yau Asabar 25 ga watan Agusta mun samu rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nufi babban birnin kasar nan na Tarayya bayan gudanar da murna ta bikin babbar Sallah a mahaifar sa ta Garin Daura dake jihar Katsina.

Hadimin shugaban kasar akan sabuwar hanyar sadarwa, Bashir Ahmad, shine ya bayyana hakan a shafin sa na zauren sada zumunta na Twitter.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar APC za ta yi nasara a Zaben 2019 - Buhari ya yi bugun Gaba

NAIJ.com ta ruwaito cewa, shugaban kasar a ranar Juma'ar da ta gabata ya karbi bakuncin wasu kungiyoyi da suka hadar da tsaffin abokanan sa na makarata, kungiyar 'yan tireda ta jihar Kano, da kuma wakilan shugabannin kananan hukumomi na jihar Katsina.

Kazalika shugaba Buhari ya gana da gwamnoni da kuma 'yan majalisar dokoki ta tarayya na jam'iyyar sa ta APC a garin Daura yayin bikin na babbar Sallah.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Osun: PDP zasu kulla yarjejeniya tare da Omisore da sauran yan takarar kujeran gwamna

Osun: PDP zasu kulla yarjejeniya tare da Omisore da sauran yan takarar kujeran gwamna

Osun: PDP zasu kulla yarjejeniya tare da Omisore da sauran yan takarar kujeran gwamna
NAIJ.com
Mailfire view pixel