Cikin Hotuna: Aisha Buhari ta ƙaddamar da Cibiyar tallafawa Mata a Garin Daura

Cikin Hotuna: Aisha Buhari ta ƙaddamar da Cibiyar tallafawa Mata a Garin Daura

Za ku ji cewa, Aisha Buhari, Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta kaddamar da wata sabuwar cibiyar tallafawa Mata ta Daura Grassroots Women Initiave, garin Daura dake jihar Katsina domin dogaro da kai.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Nigerian ya ruwaito, Uwargidan shugaban kasar da ta kaddamar da wannan sabuwar cibiya cikin garin na Daura a ranar Larabar da ta gabata, ta kuma yi amfani da wannan dama da bayar da gudunmuwar injin barar gyada domin amfanin Mata.

Cikin Hotuna: Aisha Buhari ta ƙaddamar da Cibiyar tallafawa Mata a Garin Daura
Cikin Hotuna: Aisha Buhari ta ƙaddamar da Cibiyar tallafawa Mata a Garin Daura

Cikin Hotuna: Aisha Buhari ta ƙaddamar da Cibiyar tallafawa Mata a Garin Daura
Cikin Hotuna: Aisha Buhari ta ƙaddamar da Cibiyar tallafawa Mata a Garin Daura

Cikin Hotuna: Aisha Buhari ta ƙaddamar da Cibiyar tallafawa Mata a Garin Daura
Cikin Hotuna: Aisha Buhari ta ƙaddamar da Cibiyar tallafawa Mata a Garin Daura

Cikin Hotuna: Aisha Buhari ta ƙaddamar da Cibiyar tallafawa Mata a Garin Daura
Cikin Hotuna: Aisha Buhari ta ƙaddamar da Cibiyar tallafawa Mata a Garin Daura

Hajiya Aisha take cewa, ta bayar da gudunmuwar wannan katafaren inji ne domin tabbatar da nasarar Cibiyar, inda Mata za su samu damar sarrafa gyada cikin sauki tare da shan alwashin tallafa ma su wajen kasuwanci ta hanyar shirin nan na Future Assured Programme.

KARANTA KUMA: 'Kungiyar wata Jam'iyya na goyon bayan Shugaba Buhari, ta sha alwashin kawo kuri'u 16m a Zaben 2019

Rahotanni sun bayyana cewa, Uwargidan shugaban kasar ta kuma bayar da tallafin jari ga Mata 200 domin gudanar da harkokin su na kasuwanci.

A na ta bangaren, shugaban wannan shiri na Future Assured reshen jihar Katsina, Ambaru Sani Wali, ta yabawa uwargidan shugaban kasar dangane da wannan gudunmuwa tare da kyautata Mata wajen dogaro da kai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel