Shugaba Buhari yana gudanar da manyan ayyuka a Kudu - Tsohon gwamna Kalu

Shugaba Buhari yana gudanar da manyan ayyuka a Kudu - Tsohon gwamna Kalu

Tsohon gwamnan jihar Abia, Dr Orji Uzor Kalu ya ce shugaba Muhammadu Buhari yana gudanar da manyan ayyukan gine-ginen tituna a yankin Kudu maso gabashin Najeriya a halin yanzu kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

A hirar da a kayi dashi gidan talabijin na AIT a jiya Alhamis, Kalu ya ce shugaban kasa ya fara gudanar da wasu muhimman ayyukan titi a yankin Kudu maso gabashin Najeriya kamar yadda ya yi masa alkawari yayin da zai shiga APC.

"Na tambayi shugaban kasa ya fada min abinda zai yiwa jama'an yanki na sai ya amsa da cewa zai yi musu dukkan ayyukan da zai yi a sauran yankunan Najeriya. A halin yanzu Shugaba Buhari yana gudanar da manyan ayyukan titi," inji Kalu.

Shugaba Buhari yana kwarara ayyuka a yankin Kudu - Kalu
Shugaba Buhari yana kwarara ayyuka a yankin Kudu - Kalu

DUBA WANNAN: Sabuwar rikici ta barke a jam'iyyar PDP a wata jihar Arewa

Kalu ya lissafo wasu daga cikin ayyukan da shugaban kasa ke yi wanda sun hada da: Titin Enugu zuwa Aba zuwa Fatakwal, Titin Owerri zuwa Umuahia, Titin Enugu zuwa Onitsha, Gadan Neja na biyu da sauransu.

A halin yanzu wata babban kotu a jihar Legas na tuhumar Kalu da laifin almundahanar kudade sai dai ya ce shigarsa APC bata da alaka da shari'ar da ake masa domin bai taba yin zancen da shugaban kasa ba saboda ya yi imanin yana da gaskiya kuma kotu zata wanke shi.

Kazalika, Kalu ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Progressive Alliance (PPA) ne zuwa APC saboda ba zai iya komawa jam'iyyarsa ta farko ba (PDP) saboda sun kore shi kuma har sai da ya kwashe shekaru 10 bashi da jam'iyya.

Kalu ya kuma bayyana cewa yana son jama'ar Ibo su kusanci shugaba Muhammadu Buhari

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel