Dalilin da yasa na zabi cigaba da kasancewa a APC – Shehu Sani

Dalilin da yasa na zabi cigaba da kasancewa a APC – Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani yace ya yanke hukuncin ci gaba da kasancewa a jam'iyyar APC saboda Shugaba Buhari da Oshiomhole sun sanya baki a lamarin

- Ya yi kira ga fusatattun mammbobin APC a majalisar dokokin kasar da su ajiye son zuciya sannan su hada hannu tare da jam’iyyar wajen kawo ci gaba a lamuran al’umman kasar

- Yace duk da cewar shi baya ra’ayin tikiti kai tsaye, amma dai cewa jam’iyyar tayi alkawarin yanta duk masu biyayya

Sanata Shehu Sani (APC-Kaduna ta tsakiya) ya bayyana cewa ba wai don an magance rikicinsa da shugabancin jam’iyyar na jihar Kaduna ba ne yasa shi ci gaba da kasancewa a jam’iyyar ba, sai dai saboda sanya bakin da Shugaba Buhari da shugaban jam’iyyar na kasa suka yi.

Sani ya bayyana hakan a lokacin ziyarar bikin Sallah da ya kaiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, jihar Katsina a ranar Alhamis, 23 ga watan Agusta, NAN ta ruwaito.

NAIJ.com ta tattaro cewa sanatan yayi kira ga fusatattun mammbobin APC a majalisar dokokin kasar da su ajiye son zuciya sannan su hada hannu tare da jam’iyyar wajen kawo ci gaba a lamuran al’umman kasar.

Dalilin da yasa na zabi cigaba da kasancewa a APC – Shehu Sani

Dalilin da yasa na zabi cigaba da kasancewa a APC – Shehu Sani

Kan ko an tabbatar masa da samun tikitin sake takara kai tsaye a 2019, Sani yace duk da cewar shi baya ra’ayin tikiti kai tsaye, amma dai cewa jam’iyyar tayi alkawarin yanta duk masu biyayya.

KU KARANTA KUMA: Babu wani shugaban kasa a tarihin Najeriya da yayi ma talaka aiki kamar Buhari

Ya bayyana cewa ya zama dole a bi ka’ida wajen kyautatawa mambobin da suka yiwa jam’iyyar biyayya.

Idan zaku tuna a baya NAIJ.com ta rahoto cewa Sanata Shehu Sani yayi barazanar barin APC kan zargin gaza magance matsalar cikin gia dake faruwa a jam’iyyar cikin shekara uku da shuka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Mutane ba su ji dadin labarin tsaida yunkurin tada jirgin saman kasa ba

Mutane ba su ji dadin labarin tsaida yunkurin tada jirgin saman kasa ba

Mutane ba su ji dadin labarin tsaida yunkurin tada jirgin saman kasa ba
NAIJ.com
Mailfire view pixel