'Kasar Afirka ta Kudu ta datse wani Babban Tarago daga 'Kasar Rasha ɗauke da muggan Makamai zuwa Najeriya

'Kasar Afirka ta Kudu ta datse wani Babban Tarago daga 'Kasar Rasha ɗauke da muggan Makamai zuwa Najeriya

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito mun samu rahoton cewa, 'yan sanda na kasar Afirka ta Kudu, sun datse wani tarogo daga kasar Rasha ɗauke da muggan makamai na kare dangi dake kan hanyar sa ta zuwa garin Legas na Najeriya.

Wannan tarago mai suna Lada, ya rasto ta tsuburin Madagascar ne kafin ya yada zango a tashar Elizabeth dake kasar Afirka ta Kudu, inda jami'an tsaro suka gudanar bincike na diddigi akan sa a ranar Lahadin da ta gabata.

'Kasar Afirka ta Kudu ta datse wani Babban Tarago daga 'Kasar Rasha ɗauke da muggan Makamai zuwa Najeriya
'Kasar Afirka ta Kudu ta datse wani Babban Tarago daga 'Kasar Rasha ɗauke da muggan Makamai zuwa Najeriya

Kakakin kamfanin wannan tarago na Transnet State Transport Company, Olwethu Mdabula, ta bayar da tabbacin masaniyar kayan da taragon su ya yo sufuri. Sai dai ta hau kujerar naki ta bayar da cikakken bayani kamar yadda jaridar AFP ta bayyana.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya gana da wasu Gwamnonin APC a garin Daura

Kakakin hukumar 'yan sanda mai gudanar da wannan bincike, Birgediya Hangwani Mulaudzi, ya tabbatar da wannan lamari yayin ganawa da manema labarai da cewar ko shakka ba bu wannan tarago makire yake da muggan makamai.

Legit.ng ta fahimci cewa, binciken hukumar 'yan sandan ta tabbatar da cewa, darajar wannan makamai da ta taragon ya dauko ta kai kimanin Dalar Amurka Miliyan 3.5.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel