Saudiyya ta garkame Limamin Makkah da ya soki dokar halalta cakuduwan maza da mata a taruka

Saudiyya ta garkame Limamin Makkah da ya soki dokar halalta cakuduwan maza da mata a taruka

- Masarautar Saudiyya ta daure alkalin Shari'a a garin Makkah

- An kulle shafin Turanci da na Larabcin Sheik Talib na kafar Tuwita

Gwamnatin kasar Saudiyya ta damke wani babban limamin haramin Makkah kuma Alkali a Makkah, Sheikh Dr. Saleh al Taleb, bayan ya gabatar da Huduba da ya soki sabuwar dokar halatta cakuduwan maza da mata a taro a kasar.

Wata kungiyar fafutukua ta yanar gizo mai lura da cin zarafin malaman Saudiya da masu wa’azi da gwamnatin keyi mai suna Prisoners of Conscience,ta bayyana hakan a ranan Lahadi cewa an damke Sheikh Talib ne bayan gabatar da wannan hudubar.

Jaridar Khaleej ta bada rahoton cewa a hudubar, Sheik Talib, ya soki cakuduwa a iktiladi tsakanin maza da mata ajnibai a tarukan shakatawa da shirye-shirye.

Duk da cewa bai soki masarutar mulkin Saudiyya a hudubar ba, an damkeshi bayan masarautar ta samar da dokan halastawa mata halartan taruka a kasar.

Bayan haka kuma, an kulle shafin Turanci da na Larabcin Sheik Talib na kafar Tuwita.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel