Atiku ya mayar da martani game da tattakin mita 800 da Buhari yayi a garin Daura

Atiku ya mayar da martani game da tattakin mita 800 da Buhari yayi a garin Daura

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya mayar da martani ga hotunan da ake yadawa na shugaban kasa Muhammdu Buhari yayin da yayi tattakin mita dari takwas a darin Daura bayan an tashi daga Sallar Idi.

Legit.ng ta ruwaito shugaba Buhari yayi wannan tattaki ne a ranar Sallah inda ya taso tun daga filin Idi zuwa gidansa dake GRA Daura a kasa, tare da dubunnan jama’an yan rakiya suna daga masa hannu suna kiran ‘Sai Baba.’

KU KARANTA: Gwamnan jihar Enugu ya kai ma Musulmai ziyara a Masallaci ya nemi ayi ma Buhari addua

wannan tattaki da Buhari yayi ya janyo cece kuce a tsakanin masoyansa da magauta, yayin da masoya ke cewa wannan alama ce dake nuna Buhari ya yi garas, su kuwa yan hamayya kira suke hakan ba zai rage farashin shinkafa ba.

Shima Atiku ya shige jerin masu tsokaci game da tattakin, inda yace shima yana gudun sassarfa akai akai, kuma yana motsa jiki sosai, don haka wannan ba wani abin ayi ta yayatawa bane.

Atikun ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter, inda ya daura hotonsa yana motsa jiki, sa’annan yace: “Abin kunya ne na roki yan Najeriya su zabe ni don kawai na ina motsa jiki, kuma ina gudu, ina kira ga PDP ta bani takara saboda ina aiki ba wai ina tafiya ba, zan samar da ayyuka ba matasa.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel