Buhari yayi takawar mita 800, Obasanjo ya buga kwallon kafa, Jonathan ya motsa jiki - Yadda shugabannin Najeriya ke motsa jikinsu (hotuna)

Buhari yayi takawar mita 800, Obasanjo ya buga kwallon kafa, Jonathan ya motsa jiki - Yadda shugabannin Najeriya ke motsa jikinsu (hotuna)

Tun bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tattaki na tsawon mita 800 daga masallain idi zuwa gidansa dake Daura a ranar babbanSallah, al’umman kasar ke ta tofa albarkatun bakunansu.

Wannan abu ya ba mutane da dama mamaki duba ga yawan shekarun shugaban kasar da kuma kallon da wasu ke yimasa na ganin bashi da cikakken lafiya.

Yadda shugabannin Najeriya motsa jikinsu (hotuna)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari lokain da yayi takawar mita 800 daga masallai zuwa gidansa na Daura a ranar babban Sallah
Asali: UGC

Sai dai irin hakan ba akan shugaban kasar bane farau domin tsoffin shugabanin kasar da dama na da hanyoyi da irin sigar motsa jiki da suke yi.

Yadda shugabannin Najeriya motsa jikinsu (hotuna)
Yadda shugabannin Najeriya motsa jikinsu
Asali: UGC

Akwai lokacin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya buga wasan kwallon kafa tare da jami’an gwamnatin jihar Ogun a lokacin bikin cikarsa shekaru 78 a duniya.

Yadda shugabannin Najeriya motsa jikinsu (hotuna)
Obasanjo a cikin tawagar da suka buga wasa a ranar bikin zagayowar haihuwarsa

Abun mamaki sai gashi duk da tsufar sa, tsohon shugaban kasar ya yi nasarar jefa kwallaye biyu a raga.

Yadda shugabannin Najeriya motsa jikinsu (hotuna)
Obasanjo yayinda yake jefa kwallo a raga

Haka zalika tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba’a bar shi a baya ba wajen motsa jiki inda yake launin motsa jiki mai suna Jogging a turane.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fusatattun matasa sun cinna wa kotun majistare wuta a Imo

Yadda shugabannin Najeriya motsa jikinsu (hotuna)
Tsohon shugaban kasa Goodluk Jonathan tare da ayarinsa yayinda suke motsa jiki

Dukkanin shugabannin sukan jajirce wajen motsa jiki ne domin su karawa kansu kuzari da kuma gujema cututtukan zamanin musamman ma dai na bugun zuciya.

Yadda shugabannin Najeriya motsa jikinsu (hotuna)
Yadda shugabannin Najeriya motsa jikinsu

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel