Ku tabbatar kun mallaki Katin Zaɓe a matsayin Makamin ku na ƙwatar 'Yanci - Sarkin Musulmi ga Matasa

Ku tabbatar kun mallaki Katin Zaɓe a matsayin Makamin ku na ƙwatar 'Yanci - Sarkin Musulmi ga Matasa

Za ku ji cewa Mai Martaba Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar, ya gargadi matasan Najeriya akan su tabbatar sun mallaki katin zabe a matsayin makamin su na ƙwatar 'yancin na samun nasara ta jam'iyyun su da kuma 'yan takara.

Sultan na Sakkwato ya yi wannan kira ne cikin sakon sa na gaisuwar Babbar Sallar ga Musulmai, inda ya ce katin zabe shi zai tabbatar da nasarar kowane dan takara da al'ummar kasar nan ke da ra'ayin sa a zaben 2019.

Sarkin ya shawarci al'ummar kasar nan musamman matasa akan su yi watsi da duk wani makami face katin su na zaben da zai tabbatar da nasarar kowane dan takara ko jam'iyya da suke ra'ayi.

Ku tabbatar kun mallaki Katin Zaɓe a matsayin Makamin ku na ƙwatar 'Yanci - Sarkin Musulmi ga Matasa
Ku tabbatar kun mallaki Katin Zaɓe a matsayin Makamin ku na ƙwatar 'Yanci - Sarkin Musulmi ga Matasa

A kalaman sa, "idan Buhari ku ke da ra'ayi kazalika gwamna Tambuwal ko kuma wasu 'yan takara na daban, mallakar katin zabe ita kadai ce mafificiyar hanya da za ta tabbatar da hakan a kasar nan."

Ya kuma tsawatar da matasa akan kauracewa duk wani nau'i na ta'addanci ko tashin-tashina domin kuwa kiyaye rayukan al'umma shine mafi daraja sama da zaben kansa.

KARANTA KUMA: Sarki Sanusi ya jagoranci Sallar Idi, ya yi Huɗuba kan Zaman Lafiya da Soyayyar Juna

Kazalika, Sultan ya jaddada cewa Sarakunan gargajiya a kasar nan ba su da wani zabi cikin manema takara a kasar nan face ra'ayin al'umma da talakawan su.

Sarkin Musulmin ya kuma kirayi ga 'yan siyasa da kuma jam'iyyu akan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali wanda shine jigo wajen ci gaban kasa. Ya kuma yabawa hukumomi dangane da tsayuwar daka wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel