Shugaba Buhari ya bukaci shuwagabannin hukumomin tsaro na kasa su kara zage damtse

Shugaba Buhari ya bukaci shuwagabannin hukumomin tsaro na kasa su kara zage damtse

- Bayan dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro

- Yayin taron an tattauna halin da matsalolin tsaro ke ciki a fadin kasar nan

- Gwamnonin jahohin kasar nan na cigaba da daukar matakan kare kai

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin hukumomin tsaro da su kara matsa kaimi wajen tabbatar da tsaro a fadin kasar nan.

Shugaban kasar ya bayar da wannan umarni ne yayin tattaunawarsa da shuwagabannin a taron majalisar tsaro ta kasa da ya gudana a fadara shugaban kasa a Abuja jiya.

Shugaba Buhari ya bukaci shuwagabannin hukumomin tsaro na kasar nan su kara zage damtse
Shugaba Buhari ya bukaci shuwagabannin hukumomin tsaro na kasar nan su kara zage damtse

Wannan ganawa dai ta zo ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da bikin Sallah a kasar nan, yayin da ake cigaba da fuskantar kalubalen tsaro iri daban-daban a kasar baki daya.

Jahohi da dama dai sun dauki matakan da zasu tabbatar da tsaro a jahohinsu domin yin bukukuwan Sallah cikin zaman lafiya.

Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kwara ya shaida yadda suka gano shirin wasu ‘yan siyasa dake shirin tayar da hargitsi bayan da suka gano wata mota makare da wukake.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun yi bajinta, an basu lambar yabo

Jihar Yobe ma ta sanar da dakatar da zirga-zirgar ababen hawa daga karfe 10pm na daren jiya zuwa 10am na safiyar yau.

Yayin da jihar Adamawa kuma ta dakatar da zuwa ziyarar gidan Sarki da aka saba kaiwa lokutan bikin Sallah.

Ministan tsaro na kasa Mansur Dan Ali ya shaida cewa yanayin tsaro a arewa maso gabashin kasar nan har yanzu akwai sauran rina a kaba, in da ya ce “Bayan duba na tsanaki da suka yiwa sha’anin sun dauki matakin da ya dace”.

Daga cikin wadanda suka halarci tattaunawar akwai; shugaban rundunonin tsaro (CDS) Gabriel Olonisakin, mai bawa shugaban kasa shawara kan kan harkokin tsaro Babagana Monguno da shugaban rundunar Soji Tukur Buratai.

Ragowar sune; shugaban Sojin ruwa Ibok Ekwe Ibas, shugaban Sojin sama Abubakar Sadique, babban daraktan hukumar leken asiri ta kasa Ahmed Abubakar, da mukaddashin daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) Matthew Seiyefa tare da babban Sufeton ‘yan sanda na kasa Ibrahim Idris.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel