Abin tsoro: Mahaukaci ya kashe Basarake ta hanyar soka mashi wuka a wuya

Abin tsoro: Mahaukaci ya kashe Basarake ta hanyar soka mashi wuka a wuya

- Mahaukaci ya aika sarkin garinsu lahira ta hanyar caka masa wuka a wuya

- Ana kyautata zaton cewa mahaukacin tsatson masarautar garin ne

- Jami’an tsaro na ‘yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin kuma suna kan bincike

An jefa al’umar garin Odo-Oro-Ekiti, da ke a karamar hukumar Ikole, jihar Ekiti cikin rudani da zaman makoki, bayan da aka kashe Sarkin garin, Oba Gbadebo Ogunsakin, da tsakar rana, ta hanyar caka masa wuka a wuya.

Legit.ng Hausa ta samu rahoto cewa, wani da ake kyautata zaton mahaukaci ne ya burmawa Basaraken wuka a wuyansa jim kadan bayan kamala taron majalisar masarautar.

Wani mazaunin yankin da lamarin ya faru, Henry Olu, yace wanda ya aikata wannan aika-aikar shima ya fito ne daga tsatson masarautar.

Abin tsoro: Mahaukaci ya kashe Basarake ta hanyar soka mashi wuka a wuya
Abin tsoro: Mahaukaci ya kashe Basarake ta hanyar soka mashi wuka a wuya

Rahoton ya ruwaito Mr. Olu yana cewa anga wanda ya aikata kisan gabanin fara zaman majalisar masarautar, yana zaune saman karagar sarkin, inda aka fatattake shi daga wajen a guje.

KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NECO ta fitar da sakamakon jarabawar SSSCE

Sarkin ya gamu da ajalinsa ne bayan da mahaukacin ya caka masa wuka a wuya, a lokacin da yake kokarin shiga motarsa, bayan kammala zaman majalisar masarautar.

“Iya abinda muka ji shine Ihun direban sarkin yana neman agajin jama’a, jim kadan bayan kamala zaman majalisar masarautar. A lokacin da muka isa wajen, mun taras da sarkin kwance cikin jinni, ga wuka a saman makogoronsa.

“Munyi kokarin kaishi asibiti, amma kafin a isa Oba Ogunsakin yace ga garinku nan” cewar wani da lamarin ya afku a gaban idanunsa.

A cewar rahoton, wasu matasa da lamarin ya harzuka su, sun bazama neman mutumin, wanda ake tunanin ya tsere da ya ji ana neman sa. Matasan sun shiga lungu da sako na garin suna nemansa amma basu dace ba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Ekiti, Caleb Ikechukwu, ya bada tabbacin afkuwar lamarin, ya na mai cewa “Gaskiya ne lamarin ya faru kuma yanzu haka rundunar ‘yan sanda sun shiga cikin lamarin.

“Wanda ake zargi da aikata kisan yana da tabin hankali, kuma gaskiya ne ya tsere cikin daji bayan da ya aikata kisan gillar.”

Domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel