Dole kanwar naki: Najeriya ta bada kai bori ya hau

Dole kanwar naki: Najeriya ta bada kai bori ya hau

- Najeriya ta tsallake rijiya da baya game da hukuncin dake shirin hawa kanta sakamakon rikicin shugabanci a hukumar kula da kwallon kafa ta kasa

- 'Yan mintuna kalilin ne suka rage kafin wa'adin lokacin da aka bawa Najeriya ya kare

Ba shiri gwamnatin Najeriya ta ambata sanarwar amincewa da tabbataccen shugabancin hukumar kula da kwallon kafa ta kasa ( NFF ) karkashin Amaju Pinnick.

Dole kanwar naki: Najeriya ta bada kai bori ya hau
Dole kanwar naki: Najeriya ta bada kai bori ya hau

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa, Laolu Akande mashawarcin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twita yau Litinin.

Akande ya wallafa sanarwar ne a shafin nasa da milasin karfe 11.38 a.m na safe, ‘yan mintuna kadan kafin wa’adin 12 p.m na rana ya cika da FIFA ta bayar. Sannan ya ce tuni Najeriya ta sanar da FIFA matakin daukar wannan hukunci.

“Gwamnatin tarayya ta riga da ta sanar da hukumar FIFA cewa ta yarda Amaju Pinnick ne shugaban NFF. Najeriya zata cigaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki wajen warware duk wata matsala akan lokaci." Kande ya bayyana.

KU KARANTA: Babu gwamnatin da tayi abunda Buhari yayi - Clark

Tun farko dai hukumar dake kula da kwallon kafa ta duniya (FIFA) ce ta bawa Najeriya wa’adi da zai kare yau Litinin da misalign karfe 12:pm na rana don samar da matsaya ga rikicin shugabancin NFF da taki ci ta ki cinyewa.

Wanda gaza bin wancan umarni zai janyo a dakatar da Najeriya daga shiga cikin harkokin wasanni.

Kafin bayyana wannan sanarwa dai an sha samun rahotan yiwa gidan Amaju Pinnick kawanya daga magoya bayan Chris Giwa tare da taimakon jami’an ‘yan sanda da na DSS.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel