Kalli Jaririyar farko da aka haifa a filin Arfa a hajjin bana (hoto)

Kalli Jaririyar farko da aka haifa a filin Arfa a hajjin bana (hoto)

Ranar yau, Litinin, 20 ga watan Agusta yayi daidai da ranar da daukacin al’umman Musulmi ke hawan Arfa a kasa mai sauki.

Rahotanni sun nuna cewa kimanin Musulmin duniya sama da miliyan biyu ne suka hallara a wannan fili na Arfa inda suke kara neman kusanci ga Allah Madaukakin sarki atre da yin tasbihi.

Wannan rana na da matukar muhimmanci ga Musulman duniya baki daya.

Don haka muke kawo maku labarin wata jaririya da ta dace da falalar wannan rana, domin an haife ta a filin na Arfa.

KU KARANTA KUMA: Kasafin kudin 2019: Saraki ya caccaki bangaren zartarwa yace bata da tanadi

A cewar shafin BBC Hausa, wani malamin Musulunci mai suna Shaykh Mohammed Aslam ne ya wallafa hoton jaririyar a shafinsa na Facebook inda yace ita ce jaririyar farko da aka Haifa a asbitin da ke filin Arfa kuma a ranar Arfa.

Ga hoton a kasa:

Kalli Jaririyar farko da aka haifa a filin Arfa a hajjin bana (hoto)
Jaririyar farko da aka haifa a filin Arfa a hajjin bana

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel