Da duminsa: ‘Yan majalisa sun tsige shugaban karamar hukuma a Kebbi

Da duminsa: ‘Yan majalisa sun tsige shugaban karamar hukuma a Kebbi

An tsige Umar Musa Basse, shugaban karamar hukumar Koko Besse dake jihar Kebbi, kamar yadda Yusuf Gobir, shugaban majalisar kansilolin karamar hukumar ya tabbatar wa da manema labarai a jiya, Lahadi, a birnin Kebbi.

Ya kara da cewa ‘yan majalisa 10 daga cikin 12 sun saka hannu a kan takardar tsige shugaban karamar hukumar a ranar 17 ga watan Agusta.

A cewar Gobir, shugaban karamar hukumar ya aikata manyan laifuka guda 8 da suka hada da cin hanci da almundahana da kudin jama’a.

Da duminsa: ‘Yan majalisa sun tsige shugaban karamar hukuma a Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu
Asali: Depositphotos

Bayan zarge-zargen da ake yiwa shugaban karamar hukumar sun girmama sai muka ba shi dammar ya bayyana a gabanmu domin yak are kan sa cikin kwana 14 amma ya yi burus da wannan dama da muka ba shi. Hakan ya saka bamu da wani zabi day a wuce mu yi amfani da ikon da doka ta bamu ta hanyar yin amfani da rinjayen ‘yan majalisar kansiloli domin tsige shi,” a cewar Gobir.

DUBA WANNAN: APC ta lissafa zunuban Saraki 6 da suka zubar da mutuncinsa a idon 'yan Najeriya

Laifukan Basse da Gobir ya lissafa sun hada da; karkatar da tan 30 na shinkafa da gwamnatin jihar Kebbi ta bayar tallafi domin rabawa jama’a lokacin azumi, karkatar da N1,700,000 domin tallafi ga rijistar masu zabe, karkatar da kujerun aikin Hajji guda da sauran wasu laifukan

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel