Na Annabi basu karewa: Wani mutumi da ya shahara wajen mayar da kayan daya tsinta

Na Annabi basu karewa: Wani mutumi da ya shahara wajen mayar da kayan daya tsinta

Duk lalacewar al’umma, ba duka aka zama daya ba, saboda duk runtsi ba’a rasa yan kwarai irin albarka ba, anan ma wani mutumi ne mazaunin garin Abuja, Ephraim Luka ya ciri tuta wajen aikata aljeri, wanda hausawa ke yi masa kirari da gadon barci.

Duk da cewa Luka talaka ne, kuma aikin dayake yi bai taka kara ya karya ba, amma hakan bai hana shi mayar da wayoyin da ya tsinta ga masu su ba, ko agoguna, katin cire kudi, kudade da muhimman takardu, bai taba kyashin hana masu kaya kayansu ba.

KU KARANTA: Babbar Sallah: Matar Gwamna Kashim Shettima ta yi rabon raguna 100 ga Malamai da gajiyayyu

Na Annabi basu karewa: Wani mutumi da ya shahara wajen mayar da kayan daya tsinta

Ephraim Luka

Daily Trust ta ruwaito Luka yana cewa wannan hali nasa baiwa ce da Allah ya bashi, musamman ta yadda yake tsintar kayayyakin, wanda sau da dama ba kowa zai iya ganin kayan ba, amma shi sai Allah yana nuna masa koda dare koda rana.

“Ni kaina ban san yadda hakan ke faruwa ba, idan ina cikin tafiyata, sai kawai na dinga ganin wayoyi masu tsada a kasa, sai na dinga mamakin ya aka yi sauran jama’an basu ga wayar ba sai ni, daga nan sai kawai na dauka na nemi mai shi, na bashi abinsa.” Inji Luka.

Da aka tambayeshi ko nawa ne adadin kayan tsintuwar da ya mayar ma masusu, sai yace “Gaskiya ban san adadinsu ba, ni kaina na manta, suna da yawa, ta dalilin haka na yi abokai da dama.”

Majiyar NAIJ.com ta jiyo shi yana cewa sau da dama yana kai kayan ne zauren ‘Hembelembe’, wani shiri da ake yi a wani gidan rediyo dake Auja, don yin cigiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Babban buri na PDP ta lashe kowane zabe a 2019 - Inji Ahmad Makarfi

Babban buri na PDP ta lashe kowane zabe a 2019 - Inji Ahmad Makarfi

Duk wanda ya iya allon sa: Ban da ‘Dan takara a zaben 2019 –Makarfi
NAIJ.com
Mailfire view pixel