Yan Nigeria 700 ne suka nutse a bahar Rum

Yan Nigeria 700 ne suka nutse a bahar Rum

Wata kungiya dake fafutukar wayar da kan'yan Nigeria dangane da illolin yin kaura zuwa kasashen ketare (MEPN), ta koka dangane da nutsewar wasu yan Nigeria 700 a tekun Rum, a kokarin su na ketare kasar zuwa wasu kasashen waje, cikin watanni shida da suka gabata.

Daraktan MEPN, Femi Awoniyi, wanda ya bayyana wannan damuwar tasu a yayin ganawa da manema labarai a Abuja, ya ce adadin su ya gaza da wadanda suka mutu a kokarinsu na barin kasarnta cikin sahara.

Da ya ke bayyana cewa Nigeria ce mafi yawan masu kaura daga Africa zuwa wasu kasashe turai don neman abin duniya, ya kuma bayyana cewa mutanen Nigeria ne aka fi tsana da hantara a kasashen turan.

KU KARANTA WANNAN: Na kusa da Buhari na Matsa Masa Lamba akan ya Mayar da Lawan Daura shugaban DSS

A cewar sa, kungiyar MEPN ta nanfafutar wayar da kan jama'a ne dangane da illoli da hatsarin dake tattare da ketare kasa ba bisa ka'ida ba, tare da karyata ikirarin cewa ana samun alatun duniya da ayyuka masu gwabi a kasashen turan.

A cewar sa: "Ko a wannan shekarar kadai, sama da mutane 1,500 ne suka nutse a tekun Rum, da yawansu 'yan Nigerian ne.

"A hakan ma ba'a kiragawa da masu mutane tanhabyar barin kasar ta ciikin sahara, ko ta kasashen da ke makwaftaka damu. Ga wadan da sukayi nasarar shiga kasashen turai, zasu tarar da kalubalen samun wurin kwana da aikinyi na jiransu."

Domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel