Masana shari'a sun bayyana adadin 'yan majalisun da za su iya tsige Saraki

Masana shari'a sun bayyana adadin 'yan majalisun da za su iya tsige Saraki

Manyan lauyoyi a Najeriya kuma masana kundin tsarin mulkin kasar sun kawo karshen cece-kucen da ake ta yi tare da muhawara game da adadin yawan 'yan majalisar dattawan kasar da za su iya tsige shugaban majalisar Dakta Bukola Saraki.

Manyan masanan da suka yi wannan fashin bakin dai su ne Mr. Femi Falana (SAN), Wole Olanipekun (SAN), Ifedayo Adedipe (SAN), da kuma Chief Mike Ozekhome (SAN) a lokacin da suke zantawa da wakilin majiyar mu ta Punch.

Masana shari'a sun bayyana adadin 'yan majalisun da za su iya tsige Saraki
Masana shari'a sun bayyana adadin 'yan majalisun da za su iya tsige Saraki

KU KARANTA: Zan maida albashi mafi karanci Naira dubu 100 - Dan takarar Shugaban kasa

Legit.ng dai ta samu cewa lauyoyin sun yi tsayuwar daka inda suka bayyana cewa dole ne sai akalla Sanatocin da suka kai 73 sun amince da tsige Saraki ne sannan har hakan zata kasance kamar dai yadda dokar majalisar Sashe na 50 sakin layi na (C) ya bayyana.

Su ma dai Lauyoyi irin su Kayinsola Ajayi (SAN), Fidelis Oditah (SAN), Mr. Norrison Quakers (SAN), Mr. Roland Otaru (SAN) da Prof. Itse Sagay (SAN) duk sun tafi ne da wannan ra'ayin.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Benue dake a arewacin Najeriya ya bayyana cewa tun da ya fice daga APC ya koma PDP yake ta fuskantar matsalolin rayuwa da kunci sakamakon irin yadda hukumomin gwamnatin tarayya ke yi masa bita-da-kulli,

Gwamna Samuel Ortom na Benue din ya bayyana hakan ne a lokacin da yake fira da wakilin majiyar mu na Vanguard lokacin da yake ansa tambayoyi daga gare shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel