Mutane Miliyan Biyu ne Ake Saran Zasuje Aikin Hajjin Bana - Hukumar Saudi

Mutane Miliyan Biyu ne Ake Saran Zasuje Aikin Hajjin Bana - Hukumar Saudi

Hukumar Saudiya ta ce akalla mutane miliyan Biyu ne daga fadin duniya ake sabran zasu hadu a birnin Makka dama garuruwan dake makwaftaka dashi a birnin saudiya don gudanar da aikin Hajjin bana, wanda za'a fara a ranar Lahadi.

Aikin Hajji, wanda yana daya daga cikin shika shikan musulunci guda biyar, ya jaba akan kowane musulmi ya gudanar dashi koda sau dayane a rayuwarsa madamar yana da halin yin hakan.

Za'a kammala aikin hajjin ne a ranar Alhamis.

A yayin aikin Hajjin, maza na sanya fararen tufafi, yayin da suma mata ke sanya fararen kaya (Harami) amma an haramta masu yin kwalliya da sanya sarkokin gwal.

Dukkan maza da matan na gudanar da aiki iri daya don samun haduwar kawunan musulmi, da nuna rashin banbanci da kuma tuba daga laifukan da suka aikata.

KU KARANTA: Gwamnan da ya koma PDP bayan fita daga APC na shirin tsallakawa SDP

A cewar alkaluman da hukumar Saudiya ta fitar, sama da mutane 750 suka rasa rayukansu a wajen jifar Shaidan a garin Mina kusa da Makka shekaru Uku da suka wuce.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa a shekara ta 2017, mutane Miliyan 2.4 ne sukayi aikin Hajji.

A cewar rahotanninna alkaluman lissafi da kamfanin labarai na Al Jazeera ta wallafa, kasar Masar mai mahajjata 108,000, itace kasar datafi yawan mahajjata a yankin Africa a 2017, duk da cewa itace ta biyar a jadawalin sunayen.

Mutane Miliyan Biyu ne Ake Saran Zasuje Aikin Hajjin Bana - Hukumar Saudi
Mutane Miliyan Biyu ne Ake Saran Zasuje Aikin Hajjin Bana - Hukumar Saudi

Sauran kasashen sun hada da Indonesia, sai India, Pakistan da Bangladesh a jerin jadawalin.

Nigeria mai mutane 79,000 tazo ta 10 a jadawalin sunayen kasashe a 2017, inda Iran ta biyo bayanta da kuma Turkiya.

Algeria nada mahajjata (36,000) yayin da Morocco keda (31,000).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel